PDP ta samu gagarumin karuwa: Yan Jam'iyyar APC 100,000 sun sauya sheka zuwa PDP

PDP ta samu gagarumin karuwa: Yan Jam'iyyar APC 100,000 sun sauya sheka zuwa PDP

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya tarbi kimanin mutane 100,000 da suka sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyarsa a karamar hukumar Zurmi da Shinkafi na Jihar.

A wani jawabi da mai magana da yawun gwamnan, Zailani Bappa, ya rattafa hannu, yace wadanda suka sauya sheka sun koma jam’iyyar PDP ne domin marawa Matawalle baya domin cigaban gwamnatisa.

Wadanda suka sauya shekar sun bayyana cewa sun yanke shawarar komawa PDP ne domin su tabbatar da nasarar da gwamna0n ke samu wajen tabbatar da zaman lafiya da cigaban Jihar.

A jawabansu, shugaban karamar hukumar Zurmi, Auwalu Bawa da tsohon ciyaman din karamar hukumar Shinkafi, Usman Ajiya sun bayyana biyayyar mutane ga gwamnatin Matawalle.

Gwamna Matawalle, a yayin da yake bayyana farin cikinsa kan suaya shekarsu zuwa jami’yyarsa, ya dau alkawarin farantawa kowa rai a Jihar.

Yace gwamnatinsa zatayi aiki taga cewa zaman lafiya ya watsu a jihar, Sannan zai cigaba da aiki wajen ganin cewa jihar ta cigaba.

PDP ta samu gagarumin karuwa: Yan Jam'iyyar APC 100,000 sun sauya sheka zuwa PDP
Matawalle
Asali: Facebook

A bangare guda, A ranar Litinin ne shugaban karamar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara, Aminu Mudi ya sanar da sauya shekarsa daga jam'iyyar APC zuwa PDP a jihar. An zabi Mudi ne kusan shekara daya da ta gabata karkashin jam'iyyar APC tare da kansiloli goma.

Ya ce komawarsa jam'iyyar ta biyo bayan hukuncin da majalisar zababbunsa ta bayyana na barin jam'iyyar da ta kawo su matsayinsu.

"Mun matukar gamsuwa cewa gwamnatin PDP din karkashin Alhaji Bello Matawalle tana kokari wajen tabbatar da ci gaban jihar mu.

"Gwamnan ya matukar yin kokari wajen dawo da zaman lafiya ga yankunan jihar ballantana kauyuka inda noma da sauran kasuwanci suka gagara a shekarun baya."

"A matsayinmu na masu son ci gaba da zaman lafiya a jihar mu, mun zauna tare da duba kokarinsa tare da mabiyansa inda muka yanke hukuncin shiga cikinsu don kawo canji na gari," shugaban karamar hukumar ya bayyana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel