Jami'ar jihar Kaduna ta sallami dalibai 80 kan laifin satar amsa

Jami'ar jihar Kaduna ta sallami dalibai 80 kan laifin satar amsa

Jami'ar jihar Kaduna KASU ta bayyana cewa ta sallami daliban makarantar 80 kan laifin satar amsa a kakar 2018/2019 da ya gabata.

Shugaban gidan karatun Kafanchan, Farfesa Ahmed Ahmed, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba wajen taron maraba da rantsar da sabbin daliban da suka samu shiga jamiar a sabuwar kakar 2019/2020.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ta ruwaito cewa an gudanar da taron maraba ga sabbin daliban a sassan Jami'ar biyu na Kaduna da Kafanchan a lokaci guda.

Farfesa Ahmed ya bayyana cewa daga cikin dalibai 80 da Jami'ar ta sallama, 10 daga cikinsu yan sashen Kafanchan ne kuma abin takaici ne dubi ga yadda ana rububin nemar shiga Jami'ar.

Yace“Duk da cewa dalibai masu neman shiga makaranta na kara yawa kowace shekara, da kalubalan da ake fuskanta, abu mafi takaici shine lamarin satar amsa.“

“A kakar 2018/2019 kadai, kimanin dalibai 80 aka kora daga jamiar kan laifukan satar amsa a jarabawa, 10 cikinsu yan sashen Kafanchan ne.“

“Wannan abin takaici ne, dubi ga yadda ake rububin neman shiga jamiar karatu.“

Ya kara da cewa jami'ar na fama da matsalar yan kungiyar asiri da kuma ta'amuni da muggan kwayoyi da haramtattun kayan shaye-shaye.

A cewarsa “Yayinda zakuyi rantsuwar shiga jami'ar da safen nan, ina mai tunatar da ku cewa KASU ba ta lamuntan dukkan wadannan laifukan da na ambata kuma ku kiyayi hakan.“

“Ku mayar da hankali kan karatuttukanmu, saboda abin da ya kawo ku kenan. Ina mai muku fatan alheri.“

Mataimakin shugaban jamiar, Yohanna Tella, wand aya wakilci shugaban, Muhammad Tanko, ya bayyana cewa dalibai 4,650 aka dauka wannan karon.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel