Yan sanda sun kama dan shekara 26 wanda yayi yunkurin kashe Mahaifiyarsa

Yan sanda sun kama dan shekara 26 wanda yayi yunkurin kashe Mahaifiyarsa

Yan Sanda sun kama wani matashi mai kimanin shekaru 26 mai suna Kamaldin Abu Sabo, wadda yayi yunkurin kashe mahaifiyarsa a birnin Lafia dake Jihar Nasarawa.

Kwamandan yan sandar Jihar, Mahmud Gidado Fari, ya bayyanawa manema labarai cewa mahaifiyar sa ta kai kararsa wurin yan sanda cewa danta ya dade yana barazanar kasheta ba wani dalili.

”Shiyasa muka kamashi kuma bada dadewa ba zamu kaishi kotu.”

”Ba daidai bane mutum yayi ikirarin kashe wani.Abinda ya banbanta wannan lamarin shine Mahaifiyarsa ce,” cewar Shugaban yan sandan

Yan sanda sun kama dan shekara 26 wanda yayi yunkurin kashe Mahaifiyarsa
Kamal
Asali: Facebook

A wani hira da manema labarai, Kamaldin mai zanan tatu a hannunshi na dama da tabbai a fuskarsa da jikinsa yace

”Ni mazaunin Unguwar Shendam ne a garin Lafia. Na bar makarantar gwamnati dake Keffi kuma ina sana”ar tela.”

”Banyi yunkurin kashe mahaifiyata ba kuma ban yarda da bayanan yan sanda cewa Mahaifyata ta kawo karana ba, Dan uwa na ne ya kawo kara na.”

”Ina da wannan zanan tatun ne saboda kwalliya, amma ni ba dan asiri bane.” Amma da aka tambaye shi akan tabbai na fuskarsa da jikinshi bai bada amsa ba.

Har ila yau, yan sanda sun kama mutum shida da ake zargi da aikata laifuka daban daban a Jihar.

Sun hada da Muhammad Adamu daga karamar hukumar Sabon Fegi dake birnin Lafia da Ali Aminu wadanda aka kama kan siya da siyar da wayoyin sata.

KU KARANTA Zargin Almundahanan N1.35bn Shaidu sun kara bayyana gaban kotu kan Sule Lamido

A bangare guda, Barandanci a jihar Neja ya dau sabon salo yayinda yan bindigan suka gargadi mutanen wasu garuruwan karamar hukumar Rafi su daina fita tsakanin karfe 4 na yamma zuwa 7 na safe saboda lokacin suke aiki.

Saboda haka, babu wani dan garin dake fitowa a lokutan kuma yan bindigan na cin karansu ba babbaka musamman satan shanu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel