Da duminsa: An rantsar da sabon Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Zailani

Da duminsa: An rantsar da sabon Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Zailani

Yan majalisar dokokin jihar Kaduna sun zabi Hanarabul Yusuf Ibrahim Zailani matsayin sabon kakakin majalisar a ranar Talata, 25 ga Febrairu, 2020.

An zabeshi ne kimanin awa daya bayan Hanarabul Aminu Abdullahi Shagali ya yi murabus daga kujerar.

Hanarabul Yusuf Ibrahim Zailani wanda ke wakiltar mazabar Igabi ta yamma, ya kasance mataimakin kakain majalisar kafin aka zabesa matsayin Kakaki a ranar Talata.

Zailani babban jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ne a jihar Kaduna.

Hakazalika, an nada Hanarabul Mukhtar Isa Hazo, mai wakiltar Bassawa matsayin sabon mataimakin kakakin majalisar jihar.

Tuni Magatakardan majalisar ya rantsar da su.

Tsohon kakakin majalisar wanda ke wakiltar mazabar Sabon-Gari ya yi murabus ne a safiyar Talata.

Mun tattaro cewa mambobin majalisar sun fara rattaba hannun tsigesa ne kafin ya guji abin kunya yayi murabus.

Amma har yanzu bamu samu labarin abinda ya sa ake kokarin tsigesa ba.

Aminu Shagali ya zama kakakin majalisar dokokin jihar ne a shekarar 2015 da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya lashe zabe a 2015.

Bayan karewar wa'adinsa na farko, an sake zabensa bisa ga alfarmar gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufa'i.

Da duminsa: An rantsar da sabon Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Zailani
Da duminsa: An rantsar da sabon Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Zailani
Asali: Facebook

A bangare guda, an yi kira ga yan majalisar sokokin jihar Taraba su yi gaggawa tsoge gwamnan jihar, Darius Ishaku, kan kauracewar da yayi jihar tun shekarar 2019.

Watanni biyu cir rabon da gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku, ya taka jiharsa ba kuma mutan jihar sunce yanayin gudanar da aikin gwamnatin jihar Taraba ya ja tsaya cik saboda rashin gwamnan, Rahoton Daily Trust.

Aikin shi na karshe kafin barin jihar shine gabatar da kasafin kudin shekarar 2020 ga majalisar dokokin jihar a ranar 19 ga watan Disamba 2019.

Jim kadan bayan gabatarwar, aka samu rahoton cewa ya bar Jalingo a ranar 22 ga watan Disamba 2019 kuma tun daga nan ba’a sake ganin kafarsa ba.

Gwamnan bai bar wa mataimakinsa, Alhaji Haruna Manu, rikon kwarya ba, sannan bai sanarwa yan majalisar jihar ba.

Bincike ya nuna cewa tun daga 19 ga watan disamba 2019 har yau, ba’a sake ganawar majalissar zantarwar jihar ba.

Har ila yau, ba wani aiki da yake gudana yanzu a Jalingo, mutane da yawa na jihar sun nuna damuwar su game da rashin gwamnan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel