Yanzu-yanzu: Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Aminu Shagali, ya yi murabus

Yanzu-yanzu: Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Aminu Shagali, ya yi murabus

Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Alhaji Aminu Shagali, ya yi murabus.

An bayyana cewa Aminu Shagali ya yanke shawarar murabus ne ka shirye-shiryen da wasu yan majalisar ke yi na tsige shi.

Shugaban kwamitin yada labarai majalisar, Tanimu Musa, ya bayyanawa NAN cewa Kakakin ya mika takardar murabus din sa ne a ranar Talata.

Mun tattaro cewa mambobin majalisar sun fara rattaba hannun tsigesa ne kafin ya guji abin kunya yayi murabus.

Amma har yanzu bamu samu labarin abinda ya sa ake kokarin tsigesa ba.

Aminu Shagali ya zama kakakin majalisar dokokin jihar ne a shekarar 2015 da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya lashe zabe a 2015.

Bayan karewar wa'adinsa na farko, an sake zabensa bisa ga alfarmar gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufa'i.

Yanzu-yanzu: Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Aminu Shagali, ya yi murabus
Yanzu-yanzu: Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Aminu Shagali, ya yi murabus
Asali: UGC

A bangare guda, an yi kira ga yan majalisar sokokin jihar Taraba su yi gaggawa tsoge gwamnan jihar, Darius Ishaku, kan kauracewar da yayi jihar tun shekarar 2019.

Watanni biyu cir rabon da gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku, ya taka jiharsa ba kuma mutan jihar sunce yanayin gudanar da aikin gwamnatin jihar Taraba ya ja tsaya cik saboda rashin gwamnan, Rahoton Daily Trust.

Aikin shi na karshe kafin barin jihar shine gabatar da kasafin kudin shekarar 2020 ga majalisar dokokin jihar a ranar 19 ga watan Disamba 2019.

Jim kadan bayan gabatarwar, aka samu rahoton cewa ya bar Jalingo a ranar 22 ga watan Disamba 2019 kuma tun daga nan ba’a sake ganin kafarsa ba.

Gwamnan bai bar wa mataimakinsa, Alhaji Haruna Manu, rikon kwarya ba, sannan bai sanarwa yan majalisar jihar ba.

Bincike ya nuna cewa tun daga 19 ga watan disamba 2019 har yau, ba’a sake ganawar majalissar zantarwar jihar ba.

Har ila yau, ba wani aiki da yake gudana yanzu a Jalingo, mutane da yawa na jihar sun nuna damuwar su game da rashin gwamnan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel