Boko Haram: Minista ta bayyana dalilin da yasa Buhari ya yafewa yan Boko Haram

Boko Haram: Minista ta bayyana dalilin da yasa Buhari ya yafewa yan Boko Haram

Ministar walwala, jinkai da harkokin jin dadin al’umma, Sadiya Umar Faruq, ta bayyana dalilin da yasa Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi afuwa ga wasu daga cikin yan Boko Haram masu tayar da kayar baya.

Bisa ga bayaninta, an yafe musu ne saboda ana bukatar suyi tunani su bar ta’adanci ta yadda za’a basu taimako a wurare daban daban na cigaban rayuwa.

Sadiya Umar Faruq ta bayyana hakane lokacin ta karbi bakuncin wakilan Shugaban hafsoshin tsaro, Janar Abayomi Gabriel Olonishaki, karkashin jagorancin kwamandan rundunar atisayi Operaton Safe Corridor, Janar Bamidele Shaffa a Abuja.

A jawabin da mataimakin darektan sadarwan ma’aikatar, Rhoda Ishaku Iliya, ya rattafa hannu, Minista Sadiya tace: ”A cikin kokarin da gwamnatin Buhari take na cimma burinta a wurin kawar da rashin tsaro da masu tayar da kayar baya, gwamnatin tarayya ta kaddamar sa shirin afuwa ga yan Boko Haram da suka tuba domin sauya tunaninsu ta yadda za’a basu taimako a wurare daban-daban na cigaban dan Adam.”

KU KARANTA Dokar hana Babur: Nakasassu sun yi zanga-zanga a gidan gwamnatin Legas

Ta yabawa jajircewa da kokarin rundunar wajen kokarin kawar da kalubalen rashin tsaro da wadannan masu tayar da kayar baya da kuma dawo dasu cikin hayyacin su.

Ta kara da cewa wannan al’amari yana da matukar mahimmanci musamman a Arewa maso gabas a yau.

A nasa bangaren, Shaffa yace: ”Dukkansu suna lafiya a garuruwansu kuma babu wani karar rashin jituwa akansu ko kuma wani korafi da aka kawo akansu.”

Ya kara da cewa ba wani shirin shigar dasu aikin soja kamar yadda wasu suke yadawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel