Kai tsaye: Kotu ta kama tsohon kakakin PDP da laifin almundahanan N400m, ana kan yanke masa hukunci

Kai tsaye: Kotu ta kama tsohon kakakin PDP da laifin almundahanan N400m, ana kan yanke masa hukunci

Babbar kotun tarayya dake Abuja, a ranar Talata, ta kama tsohon kakakin jamiyyar Peoples Democratic Party PDP, Olisah Metuh, da kamfaninsa, Destra Investments Limited, da laifi daya cikin bakwai da hukumar EFCC take zarginsa da su.

Yanke hukunci kan zargi na farko, Alkali Okong Abang ya yanke ceewa tsohon mai baiwa shugaban kasa shawarar tsaro, Sabo Dasuki, ya baiwa Olisah Metuh kudi N400m a Nuwamba, 2014.

Alkalin ya bayyana cewa ya kamata Olisa Metuh da kamfaninsa su sani cewa kudin haram aka basu saboda ba su da wata alaka da ofishin mai baiwa shugaban kasa shawarar tsaro.

Alkali Okong Abang ya yi watsi da jawabin lauyoyin Metuh na kan cewa ba zaa iya kamashi da laifi ba tunda har yanzu ana shariar Sambo Dasuki da ya bashi kudin.

A yanzu haka, Alkalin na cigaba da karanto shariarsa kan sauran laifuka shida da ake zargin Olisa Metuh da su.

Kai tsaye: Kotu ta kama tsohon kakakin PDP da laifin almundahanan N400m, ana kan yanke masa hukunci
Olisa Metuh
Asali: UGC

A shekarar 2018, Tsohon mai magana da yawun jam’iyyar PDP, Olisa Metuh, yace a shirye yake da ya mai dawa gwamnatin tarayya kudin da ya karba daga ofishin mai bawa shugaba kasa shawara ta fannin tsaro a lokacin gwamnatin shugaba Jonathan. Maganar ta fito daga bakin lauyan sa, Onyechi Ikpeazu (SAN) a ranar Alhamis din data gabata.

Idan ba’a manta ba a kwanakin baya majiyar mu Legit.ng ta kawo muku rahoton tuhumar da ake yiwa tsohon mai magana da yawun jami’iyyar bisa karbar miliyan 400 na kudin makamai.

Lauya bayyana cewa a lokacin da wanda yake karewa ya karba wadannan kudade bashi da masaniya akan ko na menene, inda hakan ya zama kwakwarar shaida a gaban kotu. A zaton sa kudaden sun fito ne daga hannun tsohon shugaban kasa wanda shine yake aiki a karkashinsa kuma yake wa bayani akan abubuwan da suka gudana na aiki.

Cif Metuh ya ce lokacin an gayyace shi ne a ofishin mai bawa shugaban kasa shawara ta fannin tsaro a shekara ta 2015, ya bukaci sanin daga inda kudin suka fito, kuma yace a shirye yake yanzu da ya mayar da kudaden in dai har ba an bada su don yiwa gwamantin aiki bane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel