Gwamnatin tarayya ta bada kwangilar N30bn domin ginin hanyoyi zuwa kasar Nijar

Gwamnatin tarayya ta bada kwangilar N30bn domin ginin hanyoyi zuwa kasar Nijar

Gwamnatin tarayya ta amince da kwangilar gina hanyoyi biyu daga jihar Sokoto da Jihar Jigawa har zuwa bodar da ta hada Nigeria da Niger akan kimanin N30bn.

Kwangila ta biyu kuma ta ginin haanya mai kilomita 50 ne daga Kunya na jihar Jigawa har zuwa bodar Niger, za’a gina ta akan N19.79bn.rwa a karkashin jagorancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a Abuja.

Bisa ga bayaninshi, kwangilar farkon mai kimanin N9.5bn ta ginin hanya ce mai kilomita 46 daga Balle Kurdella a jihar Sokoto zuwa bodar Niger.

Kwangila ta biyu kuma ta ginin hanya mai kilomita 50 ne daga Kunya na jihar Jigawa har zuwa bodar Niger, za’a gina ta akan N19.79bn.

Gwamnatin tarayya ta bada kwangilar N30bn domin ginin hanyoyi zuwa kasar Nijar
Gwamnatin tarayya ta bada kwangilar N30bn domin ginin hanyoyi zuwa kasar Nijar
Asali: UGC

Fashola yace an amince da kwangilar ne domin farfado da tattalin arzikin kasa da bunkasa kasuwanci, musamman na kasa da kasa a wadannan wuraren.

Yace, “Ma'aikatar aiki da gidaje ta gabatar da wani yarjejiniya akan hanyoyi. Na farko itace Belle/Kurdulla zuwa hanyar bodar Niger dake Sokoto. Za’a gina ta akan miliyan 9.576 kuma ana sa ran kammalawa a watanni 24.”

"Ta biyun itace Kunya a Jihar Jigawa zuwa bodar Niger akan biliyan 19.763.567.”

Ministar walwala, jinkai da harkokin jin dadin al’umma, Sadiya Umar Faruq, ta bayyana dalilin da yasa Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi afuwa ga wasu daga cikin yan Boko Haram masu tayar da kayar baya.

Bisa ga bayaninta, an yafe musu ne saboda ana bukatar suyi tunani su bar ta’adanci ta yadda za’a basu taimako a wurare daban daban na cigaban rayuwa.

Sadiya Umar Faruq ta bayyana hakane lokacin ta karbi bakuncin wakilan Shugaban hafsoshin tsaro, Janar Abayomi Gabriel Olonishaki, karkashin jagorancin kwamandan rundunar atisayi Operaton Safe Corridor, Janar Bamidele Shaffa a Abuja.

A jawabin da mataimakin darektan sadarwan ma’aikatar, Rhoda Ishaku Iliya, ya rattafa hannu, Minista Sadiya tace:

”A cikin kokarin da gwamnatin Buhari take na cimma burinta a wurin kawar da rashin tsaro da masu tayar da kayar baya, gwamnatin tarayya ta kaddamar sa shirin afuwa ga yan Boko Haram da suka tuba domin sauya tunaninsu ta yadda za’a basu taimako a wurare daban-daban na cigaban dan Adam.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel