Yadda Shugaba Buhari ya bada kwangiloli sama da 800 cikin shekaru 6 inji Sakataren Gwamnati

Yadda Shugaba Buhari ya bada kwangiloli sama da 800 cikin shekaru 6 inji Sakataren Gwamnati

  • Gwamnatin Muhammadu Buhari ta bada kwangiloli kusan 900 a shekaru shida
  • Sakataren Gwamnati yace FEC ta amince da sababbin tsare-tsare sama da 300
  • A watan Mayun 2015 ne aka rantsar da Buhari a matsayin Shugaban Najeriya

Abuja - Daga kafuwar gwamnatin Muhammadu Buhari a watan Mayun 2015 a Najeriya, majalisar zartarwa ta kasa watau FEC ta bada kwangiloli har 878.

Jaridar Premium Times ta fitar da wannan rahoton a ranar Talatta, 12 ga watan Oktoba, 2021.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya bayyana haka a wajen taron bitar da aka shirya wa Ministoci a farkon makon nan, a birnin tarayya Abuja.

Haka zalika majalisar FEC ta amince da tsare-tsare 319 da bayanai da tattaunawa 206 tsakanin watan Nuwamban shekarar 2015 zuwa watan Agustan 2021.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun fafata da Boko Haram, an ragargaji 'yan Boko Haram da yawa

Rahoton yake cewa Boss Mustapha bai yi karin bayani kan kwangiloli da tsare-tsaren da gwamnatin APC ta bada ko ta kawo a wadannan shekaru ba.

Buhari
Shugaba Buhari Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma mafi yawan kwangilolin da majalisarta FEC ta bada na samar da abubuwan more rayuwa ne da nufin farfado da tattalin arziki da kawo cigaban kasa.

Kwangiloli 878 a watanni 71

“Adadin kwangiloli, tsare-tsare da bayanan da majalisar zartarwa na tarayya ta bada tsakanin Nuwamban 2015 da Agustan 2021 sun kai 1, 403.”
“Daga ciki akwai kwangiloli 878, tsare-tsare 319, da bayanai da tattaunawa 206.” - Boss

Bayan gwamnatin Buhari ta zarce a mulki

Sakataren gwamnatin yace daga ranar 29 ga watan Mayu, 2019 zuwa 31 ga watan Agusta, 2021, majalisar FEC tayi zama sau 52, kuma ta amince da takardu 579.

Daga cikin takardun da aka amince da su akwai na kwangila 381, tsare-tsare 110 da bayanai 52.

Kara karanta wannan

Dan majalisa ga FG: Makuden kudi kafintoci da direbobi ke samu, a wajabta musu haraji

A cewar Boss Mustapha, wadannan alkaluma sun nuna kokarin shugaba Muhammadu Buhari na ganin an share wa al’ummar Najeriya kafin Mayun shekarar 2023.

Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta bada shawara

Rahoto ya zo maku cewa tsohuwar Ministar kudi, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta yi magana a wajen wani taron bitar da aka shirya wa Ministoci a fadar shugaban kasa.

Shugabar kungiyar WTO, Ngozi Okonjo-Iweala tace ya wajaba Najeriya ta rage tsadar kasuwanci. Masaniyar tace kasuwanci yana da matukar wahala da tsada a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel