Tattalin arziki: Ngozi Okonjo-Iweala ta ba Ministocin Buhari muhimman shawarwari
- Dr. Ngozi Okonjo-Iweala tace yin kasuwanci yana da tsada sosai a Najeriya
- Darektar WTO tayi kira ga gwamnati ta saukaka domin a bunkasa tattali
- Okonjo-Iweala ta bayyana wannan ne da take jawabi wajen bitar Ministoci
Abuja - Darekta Janar na kungiyar kasuwanci na Duniya watau WTO, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, ta yi magana game da halin tattalin arzikin Najeriya.
Ngozi Okonjo-Iweala tace akwai bukatar Najeriya ta rage tsadar yin kasuwanci domin a kwadaito da masu hannun jari su zuba kudinsu a cikin kasar nan.
Jaridar Daily Trust tace Okonjo-Iweala tayi wannan magana a lokacin da tayi jawabi wajen taron bitar da aka shirya wa Ministocin tarayya a fadar Aso Villa.
Rahoton yace tsohuwar Ministar kudin tayi magana ne ta yanar gizo, ta ba Ministocin kasar shawarwarin da za su taimaka wajen inganta tattalin arziki.
Dr. Okonjo-Iweala ta bayyana cewa dole a inganta tsaro idan ana so a jawo masu zuba hannun jari.
A jawabinta, masaniyar tattali da harkar kasuwancin tace tsadar kasuwanci a Najeriya, har ya zarce na sauran manyan kasashen wajen da suka cigaba.
Idan aka kamanta da sauran kasashen Afrika, kasuwanci a Najeriya ya fi tsada, sannan har yana nema ya zarce abin da ake kashe wa a kasashen Duniya.
Menene ya jawo wannan?
Baya ga haka, Okonjo-Iweala ta ce samar da abubuwan more rayuwa a Najeriya ya faye tsada, tace gwamnati da jami’an kwastam ne suka jawo wannnan.
Darektar ta WTO tace dakon kaya daga kamfani zuwa ga masu bukata yana cin kudi sosai a kasar nan.
Okonjo-Iweala tana ganin cunkoso da ake samu a tashohin kasar da tsadar dako suna cikin abubuwan da suka jawo kasuwanci yake da matukar wahala.
Miliyoyi za su rasa aikin yi
A ranar Asabar aka ji shugaban kungiyar masu kiwon kaji a Najeriya yana kuka game da yadda Dalar Amurka ta ke tashi, game da matsalar hatsi a Najeriya.
Kungiyar PAN tace mliyoyin mutane za su zama ba su da hanyar neman abinci idan aka yi sake. Ezekiel Ibrahim ya bayyana wannan da aka yi bikin ranar kwai.
Asali: Legit.ng