Yarinya yar shekara 13 ta jagoranci kira a kafa dokar hana mata auren wuri, Ta dira majalisa

Yarinya yar shekara 13 ta jagoranci kira a kafa dokar hana mata auren wuri, Ta dira majalisa

  • Amira Abdullahi, yar kimanin shekara 13 da haihuwa, ta jagoranci yan uwanta kananan yara wajen kira da kafa dokar hana auren wuri
  • Amira ta yi wannan kiran ne a wurin taron bikin ranar yara kanana ta duniya a zauren majalisar dokokin jihar Adamawa
  • Kakakin majalisar, Aminu Iya-Abbas, ya taya yaran murnar wannan rana, tare da tabbatar musu da cewa majalisa zata yi iya kokarinta

Adamawa - Wata ƙaramar yarinya yar kimanin shekara 13 ta yi kira da a kare rayuwar ƴaƴa mata da akewa auren wuri, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Yarinyar ta bukaci a ɗauki matakin kafa dokar kare haƙƙin kananan yara, wanda zai dakatar da iyaye daga aurar da su har sai sun kammala karatun Sakandire.

Kara karanta wannan

An kashe manoma uku a wani sabon hari da aka kai kan kauyen Filato

Wannan shine kiran da yara mata da basu cika shekara 18 ke yi, na a kafa dokar hana auran wuri.

Majaisar dokokin jihar Adamawa
Yarinya yar shekara 13 ta jagoranci kira a kafa dokar hana mata auren wuri, Ta dira majalisa Hoto: Adamawa Assembly FB fage
Asali: Facebook

Yarinyar mai suna Amira Abdullahi, yar kimanin shekara 13, kuma tana matakin karatu aji 3 a ƙaramar sakandire (JSS 3) GDSS, Luggere, ƙaramar hukumar Yola ta arewa, jihar Adamawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amira ta yi wannan kiran ne a zauren majalisar dokokin jihar yayin bikin ranar yara ta duniya.

Wace bukata Amira taje wa majalisa da ita?

Amira ta roki yan majalisan da su baiwa kudirin 'Kare hakkin kananan yara' muhimmanci wajen saurin amincewa da shi tun da ya tsallake karatun farko.

Ta ƙara da cewa da zaran an kafa dokar hana yiwa kananan yara auren wuri, zai taimaka sosai wajen dakatar da iyaye aurar da ƴaƴansu mata tun ba su kai munzali ba.

Kara karanta wannan

Hon Sha'aban: Da a yau za a yi zaben gwamna a Kano, warwas za a yi wa APC

Bugu da ƙari ta roki majalisa ta tabbatar da an samar da kariya ga yara mata daga matsalolin cin zarafi da kuma sauran abubuwan da ake aikatawa kananan yara.

Wane mataki majalisar dokokin ta ɗauka?

Da yake nasa jawabin, Kakakin majalisar dokokin jihar Adamawa, Aminu Iya-Abbas, ya taya yaran murnar zagayowar ranarsu ta duniya.

Hakanan kuma ya bayyana cewa majalisa zata yi duk mai yuwuwa wajen tabbatar da kare haƙƙin ƴaƴa mata.

A wani labarin na daban kuma Jarumai 7 da shirin 'Labarina Series' ya haskaka tauraruwarsu a masana'antar Kannywood

Kannywood na da jarumai maza da mata masu kwarewa a fannoni daban-daban, amma ba su samun damar nuna bajintarsu.

Shirin kamfanin Saira Movies ya taimaka wa wasu jarumai 7 da muka tattaro muku wajen ɗaga tauraruwarsu a Kannywood.

Asali: Legit.ng

Online view pixel