Jarumai 7 da shirin 'Labarina Series' ya haskaka tauraruwarsu a masana'antar Kannywood

Jarumai 7 da shirin 'Labarina Series' ya haskaka tauraruwarsu a masana'antar Kannywood

  • Kannywood na da jarumai maza da mata masu kwarewa a fannoni daban-daban, amma ba su samun damar nuna bajintarsu
  • Shirin kamfanin Saira Movies ya taimaka wa wasu jarumai 7 da muka tattaro muku wajen ɗaga tauraruwarsu a Kannywood
  • Shirin Labarina ya samu bada umarni daga ɗaya daga cikin hazikan daraktoci wato Aminu Saira

Kano - Masana'antar Kannywood cike take da jarumai maza da mata masu kwarewa a fannonin fim da dama amma kuma ba kowa ya sansu ba.

Legig.ng Hausa ta tattaro muku wasu jarumai 7 da suka jima ana damawa da su a kannywoid amma saida suka fito a shiri mai dogon zango 'Labarina' sannan tauraruwarsu ta haska.

Kamfanin Saira Movies ne ya shirya shirin, wanda ya samu bada umarnin Aminu Saira, kamar yadda Aminiya ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Buhari ya yi wa tsoffin sojojin Biyafara 102 afuwa, ya amince da biyansu kudin sallama

Jaruman Kannywood
Jarumai 7 da shirin 'Labarina Series' ya haskaka tauraruwarsu a masana'antar Kannywood Hoto: @Nuhuabdullahi
Asali: Instagram

Ga jaruman kamar haka:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

1. Nuhu Abdullahi

Nuhu Abdullahi yana ɗaya daga cikin matasan jarumai masu tasowa kuma an jima ana fafatawa da shi a cikin masana'antar Kannywood.

Shirin Labarina ya taimaka wajen haskaka tauraruwar Nuhu Abdullahi, wanda ya fito a matsayin 'Mahmud' kuma yana cikin taurarin fim ɗin.

2. Isa Adam Feroskan

Isa Adam wanda aka fi sani da Feroskan ya jima yana fitowa a fina-finan Hausa na Kannywood musamman masu dogon zango.

Jarumin ya fito cikin shirin Labarina a matsayin 'Presdo' kuma shirin ya yi matukar taka rawa wajen daga tauraruwarsa ga masu bibiyar Kannywood.

Isa Adam
Jarumai 7 da shirin 'Labarina Series' ya haskaka tauraruwarsu a masana'antar Kannywood Hoto: @Aminu Saira
Asali: Instagram

3. Maryam Waziri

Jaruma Maryam Waziri ta shiga zukatan masu kallon fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood bayan fitowarta a shirin Labarina.

Laila kamar yadda ta fito a shirin, tana taka muhimmiyar rawa ta azo a gani, inda ta fito a ɗiyar hamshaƙin mai kuɗi kuma gata da kirki.

Kara karanta wannan

Mun yi amfani da aikin noma wajen tsamo sama da mutum milyan 4 daga Talauci, Ministan Noma

Laila
Jarumai 7 da shirin 'Labarina Series' ya haskaka tauraruwarsu a masana'antar Kannywood Hoto: @Aminusaira
Asali: Instagram

4. Abdallah Amdaz

Jarumi Abdallah Amdaz mawaki ne kuma marubuci bayan kasancewarsa jarumi a fina-finan Hausa har da na Turanci.

Amdaz, wanda ya fito a matsayin 'Excelency' cikin shirin Labarina bai wani fice a Kannywood ba kafin ya fara taka rawa a wannan shiri.

Babu tantama rawar da yake takawa a Labarina tana taimakawa tauraruwarsa, domin ya fito a mutum mai barkwanci da ban dariya.

Amdaz da Laila
Jarumai 7 da shirin 'Labarina Series' ya haskaka tauraruwarsu a masana'antar Kannywood Hoto: @AminuSaira
Asali: Instagram

5. Yusuf Saseen

Yusuf Saseen bai jima ba sosai da shiga Kannywood, amma babu ko tantama ya shiga masana'antar da kafar dama.

Samun damar fitowa a shirin Labarina ya taimaka wajen soyiwa a zukatan makallata fina-finan Hausa, kuma duk mai kallom shirin yana jin daɗin rawan da 'Lukman' yake takawa.

6. Teemah Yola

Fatima Isa Wada, wacce mutane suka fi sani da Teemah Yola, ƙawa ga wacce aka shirya fim ɗin Labarina a kanta (Sumayya), tana taka rawar gani sosai.

Teemah ta fito a matsayin 'Rukayya' ta haska shirin sosai, inda ta taka rawa wajen fafutukar ɗora Sumayya kan hanyar gaskiya.

Kara karanta wannan

Jerin Fitattun Jaruman Kannywood 5 da suka taba fitowa takarar siyasa da kujerun da suka nema

7. Ibrahim Bala

Yusuf Bala ya jima a cikin Kannywood, kuma furodusa ne, sannan yana bada umarni amma bai yi fice ba ta yadda mutane suka san shi.

Jarumin yana taka rawar gani kasancewar ya fito a matsayin abokin Mahmud, kuma shirin ya taimaka wajen ɗaga tauraruwarsa.

A wani labarin na daban kuma kun ji cewa An Kama Ɗan Shahararren Jarumi a Masana'antar Shirya Fina-Finan India

Rahotanni na nuni da cewa hukumomin tsaro sun cafke ɗan shahararren jarumin Bollywood, Shah Rukh Khan, wato Aryan Khan.

Khan ya shiga hannun jami'an hukumar NCB ne bisa zarginsa da shan miyagun kwayoyi a lokacin wata liyafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel