Babban mota ɗauke da yashi ta yi karo da jirgin ƙasa a Kano

Babban mota ɗauke da yashi ta yi karo da jirgin ƙasa a Kano

  • Wata babban mota ɗauke da ƙasa ta yi karo da jirgin ƙasa a jihar Kano
  • Lamarin ya faru ne a safiyar ranar Talata a hanyar Ahmadu Bello Way Nassarawa GRA
  • Kwamandan FRSC na Kano ya ce tuƙin ganganci ne a ɓangaren direban ya janyo hatsarin

Jihar Kano - An shiga ruɗani a jihar Kano a ranar Laraba bayan wani jirgin ƙasa da ke tafiya ya yi karo da wani babban mota da ya ɗakko ƙasa.

Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a kan hanyar Ahmadu Bello Way, Nassarawa GRA a birnin Kano.

Babban mota ɗauke da yashi ta yi karo da jirgin ƙasa a Kano
Tippa ɗauke da yashi ta yi karo da jirgin ƙasa a Kano. Hoto: Daily Trust
Source: Facebook

Read also

Atiku Abubakar ya yi magana kan yankin da ya kamata PDP ta kai takarar shugaban kasa a 2023

Motar da ke zura gudu ya yi karo da jirgin kasar misalin ƙarfe 6 na safe, hakan ya yi sanadin direban motar ya yi rauni.

Wani shaidan gani da ido, Sama'ila Umar, ya ce babu wanda ya mutu sakamakon hatsarin illa direban mota da ya yi rauni sai kuma motar da ta lalace.

Abin da kwamandan FRSC na jihar Kano ya ce game da hatsarin?

Kwamandan FRSC a jihar Kano, Mato Zubairu ya ce tuƙin ganganci ne ya janyo hatsarin.

Ya ce:

"Da muka samu labarin hatsarin, jami'an mu sun tafi wurin sun rufe hanyar, har sai da muka kawar da tippan da taragon jirgin.
"Babu wanda ya rasa rai sai dai motar da ta lalace baki daya. Amma direban tippan yana nan lafiya.
"Abin takaici direban shekarunsa 20 ne, tabbas ƙuruciya ya taimaka wurin afkuwar haɗarin. Bai kamata mutum mai shekarunsa ya riƙa tuƙa irin wannan motar ba."

Ya kuma shawarci iyaye su guji bawa ƙananan yara motoci suna tuƙawa.

Read also

Hauka maganinta Allah: Wani mutumi ya hallaka matarsa mai kaunarsa da ɗan da suka haifa

Mutane 13 sun mutu a hatsarin mota a hanyarsu ta zuwa ɗaurin aure, ciki har da ƙanin ango da matarsa

A wani labarin daban, a kalla mutane 13 ne suka riga mu gidan gaskiya a jiya sakamakon hatsarin mota da ya faru kusa da garin Akpoku-Udufor da ke karamar hukumar Etche a jihar Rivers, The Nation ta ruwaito.

Fasinjojin da ke cikin babban bas kirar Coaster sun baro garin Afara da ke Etche a jihar, suna kan hanyarsu na zuwa hallartar wani daurin aure da za a yi a jihar Imo da ke makwabtaka da su.

Amma kasa da mintuna 30 bayan motarsu ta hau hanya, ta yi karo da wani babban mota, hakan ya yi sanadin salwantar rayyuka a kalla 13 na matafiyan.

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel