Hauka maganinta Allah: Wani mutumi ya hallaka matarsa mai kaunarsa da ɗan da suka haifa

Hauka maganinta Allah: Wani mutumi ya hallaka matarsa mai kaunarsa da ɗan da suka haifa

  • Wani mutumi, Kenneth Nwoha, ya sheƙe matarsa mai ƙaunarsa da ɗan da suka haifa, sannan ya jikkata mutanen Anguwa shida
  • Rahotanni sun nuna cewa mazauna yankin na zargin cewa mutumin ya samu taɓin kwakwalwa ne cikin kankanin lokaci
  • Kakakin rundunar yan sandan jihar Ebonyi, Loveth Odah, yace an kai mutumin asibiti domin duba cikakkar lafiyarsa

Ebonyi - Rahotanni daga jihar Ebonyi sun bayyana cewa wani mutumi ya sheƙe matarsa mai ƙaunarsa da ɗan da suka haifa, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Mutumin ya kuma fita zuwa kan titin anguwar da suke, inda ya jikkata wasu mutum shida da adda.

Mazauna yankin Isiofumini Isieke a Ebonyi inda abun ya faru ranar Talata, sun bayyana cewa sun yi matukar mamaki da abinda mutumin mai suna, Kenneth Nwoha, ya aikata.

Read also

Yan bindiga sun kashe yan sanda, Lauyoyi tare da kona fasinjojin wata mota

Jihar Ebonyi
Hauka maganinta Allah: Wani mutumi ya hallaka matarsa mai kaunarsa da ɗan da suka haifa Hoto: thenationonlineng.net
Source: UGC

A cewarsu, ba tare da tsammani ba Nwoha ya hallaka matarsa da kuma ɗansu mai shekara 6 a duniya, sannan ya fito kan hanya ya jikkata wasu shida.

Shin dama mutumin yana da ciwon hauka ne?

Wata majiya mai karfi ta bayyana cewa mazauna yajin suna tsoron cewa Mista Nwoha ya samu ciwon taɓin kwakwalwa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

A cewar majiyar, yaro ɗan kimanin shekara shida, da kuma dattijo ɗan shekara 60, suna daga cikin waɗanda mutumin ya jikkata a kan layi.

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Rahoto ya nuna cewa lokacin da mutumin ya fito kan titi ya fara farmakan mutane, yan sanda suka kariso kuma suka damke shi.

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Ebonyi, Loveth Odah, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Read also

Bollywood: An Kama Ɗan Shahararren Jarumi a Masana'antar Shirya Fina-Finan India

Yace a halin yanzu an kai wanda ake zargin asibiti domin duba lafiyar kwakwalwarsa, yayin da waɗanda suka samu raunuka aka duba lafiyarsu.

A wani labarin na daban Yan sanda sun kame waɗanda ake zargi da kisan babban malamin Addini a jihar Kano

Rundunar yan sanda reshen jihar Kano, ta bayyana cewa ta damke mutum 7 da ake zargin suna da hannu a kisan wani malami a Kano.

Kakakin yan sandan jihar, Abdullahi Kiyawa, yace mutanen sun ce, suna zargin shugaban CAN da ɓoye wani mai laifi.

Source: Legit

Online view pixel