Atiku Abubakar ya yi magana kan yankin da ya kamata PDP ta kai takarar shugaban kasa

Atiku Abubakar ya yi magana kan yankin da ya kamata PDP ta kai takarar shugaban kasa

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewa yankin da shugaban ƙasa ya fito ba shine abin damuwa ba
  • Atiku yace babu wani abu shugaban ƙasa daga kudu ko daga arewa, abinda duniya ta sani shine shugaban Najeriya
  • A halin yanzun manyan ƙusoshin jam'iyyar PDP na can suna ganawar sirri game da tsarin mulkin karba-karba

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, yace shugaban ƙasa na gaba zai iya fitowa daga kowane yanki, kamar yadda The cable ta ruwaito.

Atiku ya yi wannan magana ne ranar Alhamis a taron majalisar zartarwa (NEC) na babbar jam'iyyar hamayya PDP, wanda ya gudana a Abuja.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan yace yankin da shugaban ƙasa ya fito ba shine hanyar warware matsalolin da Najeriya ke fama da su ba.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Sojoji sun sako shahararren jarumin Nollywood da suka damke

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar ya yi magana kan yankin da ya kamata PDP ta kai takarar shugaban kasa Hoto: pulse.ng
Asali: UGC

Dailytrust ta rahoto Atiku yace:

"PDP tana da damar ɗaukar matakai a kan dokokinta da kuma yadda za'a gudanar da ita. Hakanan kuma yan Najeriya suna da damar zaban wanda zai jagorance su.

Wane yanki ya dace PDP ta kai tikitin takara?

A cewar Atiku yankin da zai fitar da ɗan takara ba shine abin dubawa ba, domin ba shine hanyar warware damuwar ƙasar nan ba.

"Yankin da shugaban ƙasa ya fito ba abin damuwa bane, kuma ba shine karshen matsaloli ba."
"Babu wani abu kamar shugaban ƙasa daga kudu ko daga arewa, abu ɗaya kowa ya sani, shugaban ƙasar Najeriya, ga Najeriya kuma na yan Najeriya."
"Matakin da NEC zata ɗauka yau, ko dai ya bamu nasara ko akasin haka. PDP na fuskantar ƙalubale da dama amma da sannu zata warware komai."

Kara karanta wannan

2023: Jigon APC da ya shiga gidan yari ya fito, yana maganar neman Shugaban kasa

Yanzu haka PDP ta shiga taron sirri

A halin yanzun NEC na jam'iyyar PDP na cikin gudanar da taro a sirrince domin tattaunawa kan matakin da kwamitin karba-karba ya ɗauka da sauran batutuwa.

Rahoto ya nuna cewa kwamitin ya yanke shawarar kai kujerar shugaban jam'iyyar PDP zuwa yankin arewa, wanda babbar alama ce PDP zata kai takara Kudu.

A wani labarin kuma kun ji cewa wani tsohon minista a Najeriya ya bayyana mutumin da yakamata APC ta tsayar takara a 2023

Tsohon minista a Najeriya, Adeseye Ogunlewe, ya bayyana cewa jigon APC, Bola Tinubu, shi ne ya fi cancanta ya gaji shugaba Buhari a 2023.

Ogunlewe ya bayyana cewa a ranar Alhamis mai zuwa za'a ƙaddamar da tawagar yaƙin neman zaɓen Tinubu reshen mahaifarsa, jihar Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262