‘Yan Sanda sun yi ram da mutum 2 da gangunan jikin wasu ‘yan makaranta da aka sace

‘Yan Sanda sun yi ram da mutum 2 da gangunan jikin wasu ‘yan makaranta da aka sace

  • ‘Yan Sandan Legas sun kama wasu mutane dauke da gawar kananan yara a mota
  • Ana zargin an sace wadannan yara ne a yayin da suke hanyarsu ta zuwa makaranta
  • Da aka yi ram da wadanda ake zargin sun hallaka yaran, wani yayi kokarin ya tsere

Lagos - Wasu mutane da ake zargi da laifin satar yaran makaranta suna hannun jami’an ‘yan sandan SCID masu binciken laifuka na reshen jihar Legas.

Daily Trust ta rahoto cewa an kama wadannan mutane biyu da kawo yanzu ba a bayyana sunayensu ba a wata unguwa mai suna kira Jibowu a Legas.

A ranar Litinin, 4 ga watan Oktoba, 2021, aka cafke wadannan mutane da buhuna dauke da jikkunan wasu yara da aka kashe a hanyar zuwa makaranta.

Read also

2023: Jigon APC da ya shiga gidan yari ya fito, yana maganar neman Shugaban kasa

Wani babban jami’in dan sanda da ke ofishin Ikeja, ya shaida wa jaridar cewa an kashe wadannan yara ne kafin dakarun ‘yan sanda su iya kai masu taimako.

Yadda abin ya faru

‘Dan sandan yace jami’ansu sun tare titi a Jibowu, sai suka ci karo da motar wadannan mutum biyu da aka samu dauke da kananan yaran da ake ta nema.

‘Yan Sanda
Dakarun 'Yan Sanda a Legas Hoto: www.thisdaylive.com
Source: UGC

Wannan jami’i yace ‘yan sandan da ke bakin aiki sun bukaci takardun motarsu, a lokacin da ake yi masu wannan tambaya, sai aka fuskanci ba su da gaskiya.

“Wadanda ake zargi sun yi yunkurin ba ‘yan sanda cin hanci da nufin a kyale su su wuce, amma jami’an suka dage a kan sai an binciki motar.”
“Sai suka gano wani buhu a cikin bayan motar. Da aka bude sai aka ga yara biyu a ciki, an daure masu hannuwa da kafafu, an rufe masu baki.”

Read also

Jerin yan arewa da Tinubu zai iya dauka a matsayin abokan takara idan ya shiga tseren shugaban kasa na 2023

An tuntubi iyayen yaran

Majiyar tace daya daga cikinsu ya yi kokarin ya tsere, amma aka cafko shi. An wuce da direban da mai zaman banza a motar, da gawar yaran zuwa ofishin SCID.

Wani ‘dan sanda da ke aiki a sashen kisan-kai a garin Ikeja ya fada wa manema labarai cewa tuni an tuntubi iyayen yaran domin su zo su dauki gawar ‘ya ‘yansu.

A makon nan ne aka ji cewa rigimar Femi Fani-Kayode da uwar ‘ya ‘yansa, Precious Chikwendu ta cabe, magana ta kai gaban kwamitin majalisar attawa na kasa.

Miss Precious Chikwenduta tana ikirarin Fani-Kayode yana amfani da ‘Yan Sanda ya hana ta ganin ‘ya ‘ya hudu da suka haifa a lokacin a suke tare, kafin su rabu.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel