2023: Jigon APC da ya shiga gidan yari ya fito, yana maganar neman Shugaban kasa
- Orji Uzor Kalu yace mutane sun dame shi da maganar tsaya wa takara a 2023
- Sanata Kalu ya bayyana cewa sam bai da niyyar zama Shugaban kasar Najeriya
- Babban burin tsohon gwamnan shi ne ya koma Majalisa, sai ya yi ritaya a 2027
Kebbi - Jaridar The Nation ta fitar da rahoto cewa Mai tsawatar wa a majalisar dattawan Najeriya, Orji Uzor Kalu, yace bai da niyyar yin takarar shugaban kasa.
Sanata Orji Uzor Kalu ya bayyana wannan a lokacin da yake zanta wa da ‘yan jarida a babban birnin tarayya Abuja bayan ba shi sarautar Kibiyan Argungu.
Uzor Kalu yace a halin yanzu, ba ya tunanin neman kujerar shugaban kasa, amma idan mutane suka hadu kan cewa akwai bukatar hakan, zai amsa kiransu.
Da aka tambayi Sanata Kalu ko yana sha’awar zama shugaban kasa, sai yace babu wannan a ransa. Kalu yace yana jin dadin yadda ake yin aiki a majalisa.
“Babu wannan abin a rai. Ku fahimci cewa yankuna biyu ne kurum ba za su taba samun mulki ba – yankin Kudu maso gabas da Arewa maso gabas.”
“Saboda haka ban taba tunanin tsaya wa takarar shugaban kasa ba. Amma duk inda na shiga mutane suna damu na da maganar zama shugaban kasa.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Buri na in koma majalisa har 2027
“Na fada wa abokai na a siyasa da ‘yanuwa cewa ina so in sake koma wa majalisar dattawa.”
Uzor Kalu yake cewa wa’adinsa na Sanata zai kare a 2023, kuma zai so ya zarce a kujerar. Kalu yace yana sa rai bayan zaben 2027, ya yi ritaya daga siyasa.
Jerin yan arewa da Tinubu zai iya dauka a matsayin abokan takara idan ya shiga tseren shugaban kasa na 2023
Kalu yace babu wanda ya isa ya kai kan shi kujerar shugaban kasa, dole sai ya tattauna da sauran bangarori domin ganin idan hakarsa za ta iya cin ma ruwa.
Tsohon gwamnan ya kara da cewa yana da cancanta da karfin da zai iya duk wani aiki da ‘yan Najeriya suka taru suka ba shi, ba burin wasu ‘yan tsiraru ba.
An ba Kalu sarauta a Kebbi
A baya an ji Mai martaba Sarkin Argungu, Mohammed Mera zai ba tsohon gwamnan Abia sarauta.
Haka zaika an ji cewa Mai Martaba Mohammed Mera zai nada Lai Mohammed a matsayin Kakakin Kebbi. Tuni dai aka yi wannan nadi a watan Satumba.
Asali: Legit.ng