Tsohuwar Mai dakin Femi Fani-Kayode ta kai kararsa da IGP gaban Majalisar Dattawa

Tsohuwar Mai dakin Femi Fani-Kayode ta kai kararsa da IGP gaban Majalisar Dattawa

  • Tsohuwar matar Femi Fani-Kayode ta kai rikicin su wajen Majalisar Dattawa
  • Precious Chikwendu na so kwamitin Majalisa ta binciki gallaza mata da aka yi
  • Chikwendu tace Fani-Kayode yana amfani da ‘Yan Sanda wajen ci mata zarafi

Abuja - Tsohuwar matar Femi Fani-Kayode watau Precious Chikwendu ta hada da mijinta da manyan jami’an ‘yan sanda, ta kai kararsu a majalisar dattawa.

Jaridar Punch tace Precious Chikwendu ta kai korafin tsohon mai gidanta, Sufetan ‘yan sanda, da wani kwamishinan ‘yan sanda na Abuja gaban kwamitin majalisa.

Miss Precious Chikwendu ta shaida wa kwamitin da ke lura da harkar ‘yan sanda a majalisar dattawan kasar cewa tsohon mai gidan na ta ya matsa mata lamba.

Precious Chikwendu ta kai karar ta hannun lauyanta, Abdul-Aziz Jimoh, tana cewa Fani-Kayode yana amfanni da IGP da kuma CP James Idachaba wajen gallaza mata.

Kara karanta wannan

Zamfara: Ƴan bindiga sun kashe mutum 19, ciki har da ƙananun yara, sun ƙone shaguna da gidaje

A cewar Abdul-Aziz Jimoh, tsohon Ministan yana bi ta hannun wadannan jami’an tsaron domin ya raba Chikwendu da ‘ya ‘yanta hudu da suka haifa da suke tare.

Barista Jimoh yace bayan Fani-Kayode ya hana Chikwendu ganin ‘ya ‘yanta, ta shigar da kara mai lamba CV/372/2021 a gaban kotun tarayya a watan Fubrairun 2021.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Precious Chikwendu
Precious Chikwendu da 'ya 'yanta Hoto: Instagram/Precious Chikwendu
Asali: Instagram

Chikwendu: Fani-Kayode yana amfani da 'yan sanda

“Saboda wannan kara ne Fani-Kayode ya dauko jami’an ‘yan sanda domin a ci mutuncin wanda muke kare wa, har lauyoyinta suka rubuta wa ‘yan sanda takarda.”
“A maimakon Cif Fani-Kayode ya sallama kansa a kotu, ya kare kansa kamar yadda duk wani ‘dan kasa na kwarai zai yi, sai ya shiga karar wanda muke kare wa.” - Jimoh esq.

Kamar yadda jaridar ta bayyana a jiya, Lauyan yace tsohon Ministan harkokin jiragen sama na kasa ya zargi Chikwendu da laifin yin karya da jirkita wasu takardun kotu.

Kara karanta wannan

Yobe: Mata mai juna biyu ta haɗa baki da wasu maza 2 wurin garkuwa da kanta

“Wanda muke kare wa ta shigar da kara a babban kotun tarayya, tana karar sufetan ‘yan sanda da wasu manyan ‘yan sandan da suke da hannu wajen gallaza mata.” - Jimoh esq.

Jimoh yace duk da haka ‘yan sanda ba su kyale Miss Chikwendu ba, sun cigaba da tsare ta. A karshe ya yi kira ga kwamitin ya gudanar da bincike, ya duba batun.

Hafsah Ganduje v EFCC

A jiya aka ji cewa mutanen Kano na tofa albarkacin bakinsu a kan abin da ya faru da Mai dakin gwamna Abdullahi Ganduje, inda aka ji cewa hukumar EFCC ta neme ta.

Mu’az Magaji ya yi magana a kan tirkar-tirkar Hafsat Ganduje da hukumar EFCC. Tsohon Kwamishinan nan Kano ya yi wasu maganganu a kan batun a Facebook.

Asali: Legit.ng

Online view pixel