NAFDAC ta gargadi 'yan Najeriya da su daina cin daskararrun kaji da talo-talo

NAFDAC ta gargadi 'yan Najeriya da su daina cin daskararrun kaji da talo-talo

  • Hukumar NAFDAC ta bayyana gargadi ga mutanen da ke sayen kajin kasar waje da ke zuwa a daskare
  • Hukumar ta ce, akwai illar da ke tattare da sinadarin da ake sanya wa a cikin kajin domin kada su baci
  • Hukumar ta kuma ce, sayen kajin waje zai durkusar da tattalin arzikin 'yan kasuwan cikin gida

Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) a jiya ta gargadi 'yan Najeriya da su guji cin daskararrun kayayyakin kaji da sauran kayayyakin abinci da aka adana da sinadarin Formalin.

Formalin wani sinadari ne mai guba wanda aka fi amfani da shi don adana gawa domin kada jikin mutum ya lalace, The Nation ta ruwaito.

Kakakin NAFDAC, Dakta Abubakar Jimoh, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Abuja cewa wasu mutane suna amfani da sinadarin Formalin don adana kaji da sauran nau'ikan nama.

Read also

Ko a jikina asarar da na tafka, abu daya ne ya dame ni, Zuckerberg mai kamfanin Facebook

NAFDAC ta gargadi 'yan Najeriya da su daina cin daskararrun kaji da talo-talo
Daskrararrun Kaji | Hoto: premiumtimesng.com
Source: UGC

Formalin yana da karfin adana irin wadannan samfuran abinci na tsawon makonni kafin su isa ga masu amfani dasu.

A cewar Jimoh

“NAFDAC tana fadakar da 'yan Najeriya kan wannan abu. Akwai isassun nau'ikan kaji a cikin kasar fiye da yin amfani da daskararrun kaji da aka shigo da su, baya ga haramcin Gwamnatin Tarayya."

Kakakin NAFDAC ya kuma ja hankalin masu amfani da daskararrun kajin da ake shigo dasu da su duba yanayin tattalin arzikin wajen sayen kajin cikin gida.

Ya lura cewa idan aka ci gaba da sayen kayan waje, manoman kaji da 'yan kasuwa na gida ba za su girma yadda ake so ba, saboda kudin da ake kashewa kan kayayyakin fasa-kwaurin zai tafi ne kawai ga wasu mutane a waje.

Jimoh ya kara da cewa, kula da kayayyakin da aka shigo da su daga kasashen waje ko kuma na fasa kwaurin za su ci gaba da yin illa ga taskar kudaden waje na Najeriya.

Read also

Jama’a sun shiga halin fargaba yayin da ‘yan bindiga ke kafa sansani a birnin tarayya

Bincike: Gida mai yawan mutum 4 na bukatar kashe N10k don dafa shinkafa jollof

Talakawa ‘yan Najeriya na ci gaba da shan wahalar hauhawar farashin kayan abinci, inda tukunyar daya daga cikin shahararrun abincin kasar nan, shinkafa Jollof, yanzu za a iya kashe akalla Naira 10,00 don girkawa iyali mai mutane hudu.

Wannan ya karu da kashi 39.3% ko N2,913 akan N7,401 da ake kashewa a watan Janairun 2017 don shirya irin wannan abinci.

An samar da wannan kima ne yayin da aka kimanta nazarin matsakaicin farashin kayan masarufi da ya fito daga Ofishin Kididdiga na Kasa ta a watan Agusta 2021 wanda aka zaba cikin rahoton farashin abinci da aka fitar ranar Talata, 21 ga Satumba, 2021.

Wadannan sinadaran sun hada da hadin shinkafa, tumatir, albasa, man girki, nama, kaza da naman sa.

Dangane da bayanan NBS, kowanne daga cikin abubuwan da aka ambata farashinsu a kilo I ya karu akalla da 30% a cikin shekaru hudu da suka gabata.

Read also

Tonon asiri: Yadda Stella Oduah ta wawuri N5b, ta siya katafaran gidaje a London

Nama ya kare a jihar Kwara sakamakon tsadar farashin shanu a yankin

A bangare guda, Rahoto daga Daily Trust ya ce, mahauta a jihar Kwara sun daina yanka shanu sakamakon tsadar kayan masarufi.

Wannan lamarin ya haifar da karancin nama a duk kasuwanni a Ilorin, babban birnin jihar.

Wani mahauci a Kasuwar Mandate da aka fi sani da Alfa ya ce ba za su iya samun naman da za su saya daga dukkan mahautan da ke Ilorin ba.

Source: Legit

Online view pixel