Wanda zai gaje ni sai yayi rusau da ragargazar gidaje fiye da ni, El-Rufai
- Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce wanda zai gajesa sai yayi rusau din da yafi nashi
- Gwamnan ya koka da yadda jama'a suke zaginsa kan baya tallafawa mutane ta hanyar raba kudi
- Ya ce sun fara da gyaran bangaren ilimi daga bisani suka koma hanyoyi, talakawa suna murna
Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce wanda zai gaje shi zai rufe gidaje tare da ragargajesu domin habaka jihar fiye da yadda yayi a jihar.
Ya ce wasu jama'a na kallonsa a mai rusau kuma sun kosa wa'adin mulkinsa ya kare, Daily Trust ta ruwaito.
Gwamnan wanda ya sanar da hakan a wata tattaunawa da aka yi da shi a gidajen rediyo a ranar Alhamis, ya ce mazauna jihar yanzu suna jinjina masa a kan yadda mulkinsa ke gyara birane,
KU KARANTA: Matasan arewa, 'yan majalisa sun bukaci daukan mataki kan barazanar sheke shugaban EFCC
KU KARANTA: Tsaro: Hankalina yafi kwanciya a Maiduguri fiye da Abuja, Sanata Ndume
Ya ce mulkinsa ya bada fifiko a habaka ababen more rayuwa fiye da rabawa jama'a kudi da sunan tallafi, Daily Trust ta wallafa.
"A lokacin da muka fara aiki kan gina makarantu, sun ce bamu samar da hanyoyi masu kyau ba. Yanzu muna aiki kan hanyoyi, amma suna cewa bamu tallafawa jama'a ba.
“Idan rabawa jama'a kudi da dare shine abinda ake nufi da tallafawa jama'a, su cigaba da zaginmu.
“Talakawan da muke wa aiki ai suna godiya kan abinda muke yi. Kun san zabe ya kusa kuma suna kallona a Mai Rusau.
"A tunaninsu wanda zai zo bayana ba zai rushe komai ba. Amma rusau din da zai yi musu sai ya fi ni da izinin Allah," yace.
Yayi kira ga jama'a da su cigaba da goyon baya tare da yi wa mulkinsa addu'ar nasara.
A wani labari na daban, 'yan ta'addan da ba a san yawansu sun halaka sakamakon ayyukan kakkabar 'yan ta'adda da sojoji suka yi a yankin kudu maso gabas da kudu kudu na kasar nan a cikin makonni biyu da suka gabata.
A ranar Alhamis ne hedkwatar tsaro tace 'yan ta'adda masu yawa dake da alaka da IPOB da ESN sun bakunci lahira, Daily Trust ta ruwaito.
Halaka 'yan ta'addan ya zo ne a samame daban-daban tsakanin 3 ga watan Yuni zuwa 16 ga watan Yuni inda aka dinga dakile miyagun ayyukan IPOB da ESN.
Asali: Legit.ng