'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane 2 su na tsaka da amsar kuɗin fansa

'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane 2 su na tsaka da amsar kuɗin fansa

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kama masu garkuwa da mutane 2 yayin amsar kudin fansa
  • Dama mahaifin yaron da su ka sata mai shekaru 7 ya kai mu su korafi tun bayan sace shi da su ka yi da tsakar dare
  • Jami’in hulda da jama’an rundunar, DSP Abimbola Oyeyemi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin

Ogun - Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta samu nasarar damkar masu garkuwa da mutane 2 su na tsaka da amsar kudin fansar yaro dan shekara 7, kamar yadda The Punch ta ruwaito,

Jami’in hulda da jama’an rundunar, DSP Abimbola Oyeyemi ne ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Litinin inda ya ce sun kama wani Muhammed Abubakar mai shekaru 42 da Clinton Niche mai shekaru 18.

Kara karanta wannan

Yobe: Mata mai juna biyu ta haɗa baki da wasu maza 2 wurin garkuwa da kanta

'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane 2 su na tsaka da amsar kuɗin fansa
Kakakin 'yan sandan jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakan ya biyo bayan korafin da aka kai ofishin ‘yan sandan na Agbara

Oyeyemi ya ce mahaifin yaron, Stephen Ajibili, ya kai korafin satar dan sa, Daniel, da aka yi inda ya ce mahaifiyar sa tana tsaka da aiki da misalin karfe 11:20am aka sace shi.

Ya kara da bayyana cewa mahaifin yaron ya bayyana mu su yadda masu garkuwa da mutanen su ka kira kuma su ka bukaci kudin fansa N1m.

Kamar yadda The Punch ta ruwaito, ya ce:

“Bayan an kai rahoton, kwamandan ‘yan sandan yankin Agbara, CSP Kayode Shedrack, ya yi gaggawar tattara rundunar ‘yan sanda don su yi gaggawar bincike da daukar mataki akan lamarin.
“Kokarin ‘yan sandan ya haifar da da mai ido don masu garkuwa da mutanen sun bukaci iyayen yaron su kai kudin fansa daga nan aka dana musu tarko.

Kara karanta wannan

Adamawa: Magidanci mai 'ya'ya 3 ya rasa ransa bayan shan guba da ya yi sakamakon rikici da matarsa

“Daga nan ne ‘yan sanda su ka tasa keyar su har sai da su ka nuna musu inda su ka daure yaron a cikin daji.
“Yayin tambayar wadanda ake zargin, sun sanar da ‘yan sanda cewa su 3 ne, dayan ya na kula da inda aka daure yaron ne yayin da su kuma su ka je amsar kudin fansa.
“Bayan fahimtar an kama mutane 2 daga cikin su, daya ya ba hammatar sa iska take yanke.”

Jami’in hulda da jama’an ya ce mukaddashin kwamishinan ‘yan sandan jihar, DCP Abiodun Alamatu, ya bayar da umarnin yin gaggawar mayar da wadanda ake zargin zuwa yankin yaki da garkuwa da mutane na bangaren binciken sirri na manyan laifukar rundunar.

NSCDC ta kama mutumin da ke taimakawa masu garkuwa karɓar kuɗin fansa

A wani labarin daban, Jami'an hukumar NSCDC a jihar Enugu sun kama wani mutum da ke aiki tare da masu garkuwa da mutane a Legas kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC za ta yaki satar kudin fanshon ma’aikata, wasu mutane sun wawuri N150bn

Danny Manuel, mai magana da yawun hukumar NSCDC a Enugu ya ce an kama mutumin dauke da katin ATM uku, wayoyin salula biyu, wani ganye da ake zargin wiwi ne da wani bindiga na gargajiya.

Ya ce sunan wanda ake zargin Manuel Oguamanam da aka kama a WTC Estate a Enugu misalin karfe 2 na rana bayan dalibai da ke dawowa daga makaranta sun hange shi yana yi wa wasu fashi da bindigarsa pistol.

Asali: Legit.ng

Online view pixel