Sheikh Gumi: Ƴan jaridan da suke kiran ƴan bindiga ƴan ta’adda ne asalin ƴan ta’addan

Sheikh Gumi: Ƴan jaridan da suke kiran ƴan bindiga ƴan ta’adda ne asalin ƴan ta’addan

  • - Sheikh Gumi ya yi wa ‘yan jaridar da suke kiran ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda wankin babban bargo
  • - Kamar yadda malamin addinin ya ce, sune asalin ‘yan ta’addan, kiran ‘yan bindiga hakan rashin adalci ne
  • - Ya yi wannan furucin ne a wata tattaunawa da Arise TV ta yi da shi inda ya ce ya kamata a rungumi ‘yan bindiga

Jihar Kaduna - Sheikh Gumi, babban malamin addinin musuluncin nan na Kaduna ya ce ‘yan jaridar da suke kiran ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda ne asalin ‘yan ta’addan.

Kamar yadda Arise News ta ruwaito, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da gidan Talabijin din Arise ta yi da shi, ya ce akwai buƙatar a rungumi ‘yan bindiga a al’umma.

Read also

'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane 2 su na tsaka da amsar kuɗin fansa

Sheikh Gumi: Asalin ƴan ta'adda sune ƴan jarida da ke kiran ƴan bindiga da 'ƴan ta'adda'
Sheikh Gumi yayin da ziyarci yan bindiga a sansaninsu. Hoto: Daily Trust
Source: Facebook

Daya daga cikin mai gabatar da shirin ya bayyana yadda ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda suke yayin da ya tambayi malamin abinda suke so kafin su zubar da makaman su.

A cewar Gumi, ya kamata a rungumi ‘yan bindiga a al’umma

Yayin da Gumi yake amsa tambayar sa, ya ce 'Yan jarida ne ‘yan ta’addan kuma bai dace su kira ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda ba.

A cewarsa, yanzu haka a shirye ‘yan bindiga suke da su zubar da makaman su, amma duk lokacin da su ka ji ana yada labarai akan su, ana kiran su da ‘yan ta’adda, sai su hassala su ci gaba da gashi bisa ruwayar News Ngr.

A cewar Gumi, matsawar ana so ‘yan bindiga su dena addabar al’umma su dena kashe-kashe, wajibi ne a rungume su a kyautata mu su kamar yadda ake yi wa sauran ‘yan Najeriya.

Read also

Wajen bikin aure, Ango ya yi watsi da amaryarsa yayinda yaga tsohuwar budurwarsa

Sheikh Gumi Ya Bayyana Dalilin Da Yasa 'Yan Bindiga Ba Za Su Iya Garkuwa Da Shi Ba

A wani rahoton mai alaka da wannan, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce yan bindiga da ke adabar kasar nan suna kaunar wadanda ke girmama su tare da fahimtar halin da suke ciki, SaharaReporters ta ruwaito.

A cewar Peoples Gazette, Gumi ya bayyana hakan ne yayin da ya ke amsa tambayoyi daga wurin dalibai a wurin makala da aka yi a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a ranar Laraba.

Malamin wanda ya dade yana ziyartar yan bindiga a daji don yunkurin yin sulhu da su ya ce bai samu wani matsala ba wurin gana wa da su domin a koyaushe da 'kofa ya ke bi'.

Source: Legit

Online view pixel