Wajen bikin aure, Ango ya yi watsi da amaryarsa yayinda yaga tsohuwar budurwarsa

Wajen bikin aure, Ango ya yi watsi da amaryarsa yayinda yaga tsohuwar budurwarsa

  • Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu yayin da wani bidiyo ya bayyana na wani bikin aure
  • A cikin bidiyon, an fara gano ango zaune tare da amaryarsa kafin ya share ta don yin rawa da wata budurwa da ta halarci bikin
  • Wataƙila abin da mijinta ya yi ya bata mamaki, sai gashi itama amaryar ta fita yin rawa tare da wasu maza kafin angon ya dawo gareta

Wani ango ya ba mutane da yawa mamaki kan abun da yayi a filin rawa a wurin liyafar aurensa.

Angon da ba a bayyana ko wanene ba ya bar matarsa a inda suke zaune don yin rawa tare da wata budurwa da ta halarci bikin.

An sha ‘yar dirama a wajen liyafar aure yayin da ango ya yi watsi da amaryarsa don rawa da wata budurwa
An sha ‘yar dirama a wajen liyafar aure yayin da ango ya yi watsi da amaryarsa don rawa da wata budurwa Hoto: @lindaikejiblog
Source: Instagram

A cikin bidiyon da Lindaikeji Blog ta wallafa akan Instagram, abokan angon da sauran baƙin sun jinjina wa angon saboda matakin da ya ɗauka yayin da amarya ke kallo.

Read also

Labarin gimbiyar da ta bar masarautarsu ta auri talaka ya dauki hankalin jama'a

Da take martani a kan matakin da mijinta ya dauka, sai ita ma amaryar ta hau fita filin rawa don yin rawa tare da sauran baƙi maza da ke wajen.

A wannan lokacin ne angon ya daina rawa da budurwar sannan ya koma ga masoyiyarsa.

Kalli bidiyon a ƙasa:

Jama’a sun yi martani mabanbanta kan bidiyon

@openspeaker_1 ya ce:

"Duk ba ku fahimci abin ba, angon ya gaya wa matar ta fito su yi rawa sai ta ce, ba ta da ƙarfin yin rawa, lokacin da ta ga angon ♂️ yana girgiza, sai ta huce, ina a wurin."

@00_double_chief ya ce:

"Matsalar aure da baya karewa ya fara daga wajen liyafa... wa zai daidaita wannan wahalar yanzu"

@boxpro_ng opined:

"Kuma ita ma budurwar ta ji daɗin yin rawa da shashashan angon ...."

Read also

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa na lalata, aure ya mutu a daren farko

Hotunan wani mutum da ya auri tukunyarsa ta dafa shinkafa ya ɗauki hankulan mutane

A wani labarin, mun ji cewa wani mutum dan asalin kasar Indonesia ya janyo cece-kuce bayan ya bayyana yadda shagalin auren sa da tukunyar girkin lantarkin sa ya kasance.

Kamar yadda ya wallafa hotunan bikin, ya na sanye ne da fararen kaya na alfarma yayin da tukunyar take lullube da mayafi irin na amare kamar yadda LIB ta ruwaito.

Mutumin mai suna Khoirul Anam cikin shauki da tsananin farin ciki ya yi wallafar ya na kambama amaryar ta sa inda ya sa “Sabuwar amarya”.

Source: Legit.ng

Online view pixel