Sheikh Gumi Ya Bayyana Dalilin Da Yasa 'Yan Bindiga Ba Za Su Iya Garkuwa Da Shi Ba
- Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa 'yan bindiga ba za su iya garkuwa da shi ba saboda yana nuna musu kauna da girmamawa
- Sheikh Gumi ya bayyana hakan ne yayin da ya ke amsa tambayoyi daga dalibai a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria bayan gabatar da makala
- Malamin addinin musuluncin ya ce 'yan bindigan da shirye suke su saurari duk wanda ya nuna damuwa kan halin da suke ciki ya kuma saurare su
Kaduna - Malamin addinin musulunci mazaunin Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce yan bindiga da ke adabar kasar nan suna kaunar wadanda ke girmama su tare da fahimtar halin da suke ciki, SaharaReporters ta ruwaito.
A cewar Peoples Gazette, Gumi ya bayyana hakan ne yayin da ya ke amsa tambayoyi daga wurin dalibai a wurin makala da aka yi a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a ranar Laraba.
Malamin wanda ya dade yana ziyartar yan bindiga a daji don yunkurin yin sulhu da su ya ce bai samu wani matsala ba wurin gana wa da su domin a koyaushe da 'kofa ya ke bi'.
Ya ce:
"Ta kofa na ke shiga, ba ta taga ba. Idan ka shiga ta kofa, za ka shiga ka fito lafiya."
Gumi ya ce idan aka saurari yan bindigan, zuciyarsu za ta yi sanyi kuma hakan zai sa sufi sauya halayensu na kai hare-hare.
Da aka masa tambaya kan abin da yasa 'yan bindigan ba su yi garkuwa da shi ba duk da ziyarar da ya kai sansaninsu, Gumi ya ce:
"Idan mun hadu, ba mu magana, muna mika musu na'urar magana suyi magana na kimanin awa. Da muka hadu da su da farko, suna rike da bindigu suna shirin bude wuta. A lokacin da muka gama tattaunawa, za su mika makamansu mu dauki hotuna.
"Don haka, wannan shine darajar mu'amula da mutane wanda shi muke son yin nazari a matsayin mu na masu nazarin kimiyyan zamantakewar mutane. Wannan shine hanyar da muke bi.
"Malamin ya ce yan bindigan sun aminta da shi saboda yana daukarsu tamkar sauran 'yan adam kuma yana girmama su."
Gumi ya cigaba da cewa:
"Wannan shine girmamawar da na ke musu. Na kan ce, ku zo mu zauna tare. Ku zo ku zauna. Ina son jin abin da ke damun ku. Da irin wannan girmamawar, za ka iya nasara kan Fulani.
"Don haka kada ku yi mamaki, idan ka kyautata musu, idan ka shirya sauraronsu, idan kana kokarin gano matsalolinsu, idan ka saka kanka a matsayinsu, za su saurareka, za ka tafi daji ka dawo lafiya da izinin Allah."
Akwai Yiwuwar Malamin Addinin Musulunci Sheikh Gumi Ɗan Leƙen Asirin Ƴan Bindiga Ne, In Ji OPC
A wani labarin daban, kungiyar Yarabawa ta Oodua Peoples Congress, OPC, reshen jihar Oyo karkashin jagorancin Aare Onakakanfo na kasar Yarbawa, Gani Adams ta ce ziyarar da Gumi ya kai ta bazata jihar Oyo cin fuska ne ga Yarbawa baki daya.
A yayin zantawarsa da manema labarai a karshen mako, Rotimi Olumo, jagorar OPC a jihar Oyo ya ce Gumi yana wuce gona da iri kuma ya gargade shi ya kiyayi yankun Kudu maso Yamma na kasar Yarbawa, SaharaReporters ta ruwaito.
A cewar Olumo, ziyarar Gumi babban barazana ce ta tsaro ga dukkan yankin Yarbawa domi ba su ga amfanin hakan ba sai dai cin fuska da kokarin wofintar da mutanen kudu maso yamma.
Asali: Legit.ng