Daliban jihar Kano za su shana, Ganduje ya kara kudin da ake ba ‘Yan makaranta a duk shekara

Daliban jihar Kano za su shana, Ganduje ya kara kudin da ake ba ‘Yan makaranta a duk shekara

  • Gwamnatin jihar Kano tace an yi kari a kudin da ake raba wa ‘yan makaranta
  • Masu karatu a makarantun gaba da sakandare suna samun alawus duk shekara
  • Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta amince a kara wa daliban na Kano 50%

Kano - Gwamnatin jihar Kano ta amince a kara kudin da ake ba dalibai duk shekara. Vanguard tace an kara adadin kudin da ake raba wa da 50%.

Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana haka a wani jawabi da ya yi na somin-tabin bikin cika shekara 61 da samun ‘yancin kai daga kasar Ingila.

Kamar yadda muka samu rahoto, Mai girma Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar da lacca da aka shirya a ranar Laraba, 29 ga watan Satumba, 2021.

Muhammad Garba ya wakilci Gwamna

Read also

VAT: Gwamnonin Arewa za su hada-kai da Gwamnatin Tarayya suyi shari’a da Jihohin Kudu

Kwamishinan harkokin yada labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, ya wakilci gwamna.

Muhammad Garba ya shaida wa jama’a cewa gwamnatin Ganduje ta amince da wannan karin da aka yi, kuma za a fara biyan kudin ba da dade wa ba.

Ganduje
Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje Hoto: factualtimesng.com
Source: UGC

Kwamishinan yake cewa wannan na cikin manufofin gwamnatin Abdullahi Ganduje wanda aka sani da Khadimul Islam na bada ilmi kyauta, kuma dole.

Abdullahi Umar Ganduje ya yi kira ga daliban jihar Kano suyi amfani da wannan dama da suka samu, su maida hankali wajen samun nasara a karatunsu.

An yi sakaci da CVR a Kano

Har ila yau, gwamnan ya tabo batun rajistar katin zabe da hukumar INEC ta ke yi, ya yi kira ga ‘yan makaranta su samu damar mallakar katin yin zabe.

Read also

Jihar Niger: Mayaƙan Boko Haram sun ratsa mazaɓu 8 cikin 25, Shugaban Ƙaramar Hukuma

Ganduje yace akwai bukatar duk wanda ya isa shekaran zabe, ya samu kati kafin a rufe yin rajista.

Dr. Ganduje yace an yi wa Kano nisa a rajistan, a lokacin da aka samu mutane 400, 000 sun yi rajista a jihar Osun, mutane 100, 000 aka samu daga Kano.

Kwankwasiyya 370 sun yi kasuwa

A ranar Alhamis ake jin cewa bayan sun kammala karatu a ketare, jami’o’in waje sun rike wasu Daliban Kwankwasiyya da suka yi digirgir a kasar Indiya.

Baya ga haka, kamfanonin BUA, Dangote da Tiamin za su ba wasu daga cikin Matasan aikin yi a gida.

Source: Legit.ng News

Online view pixel