Kwankwaso: Wadanda Kwankwasiyya ta tura karatun digirgir sun samu aiki a kasar waje

Kwankwaso: Wadanda Kwankwasiyya ta tura karatun digirgir sun samu aiki a kasar waje

  • A 2019 gidauniyar Kwankwasiyya ta tura wasu karatu a UAE, Sudan da Indiya
  • Wadannan matasa sun kammala karatunsu, har sun fara samun ayyuka a ketare
  • Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa wata jam’ar Indiya ta ba yara 13 aiki

Kano - Mutane 13 daga cikin 370 da gidauniyar Kwankwasiyya Development Foundation ta tura karatu a 2019, sun samu ayyukan yi a makarantun da suka je.

Guardian ta fitar da rahoto cewa wasu mutane 13 daga cikin wadanda Kwankwasiyya Development Foundation ta ba damar karo karatu, sun samu aiki.

Da yake gabatar da mutane 370 da suka amfana da gidauniyarsu, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yace mutane akalla 13 aka rike a inda suka yi karatu, aka ba su aiki.

Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa wadannan mutane sun samu aiki ne saboda hazakar da suka nuna a wajen karatun na su.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya yi iƙirarin wasu manya sun daƙo hayar masu kisa daga ƙasar waje su kashe shi

Jaridar ta rahoto Kwankwaso ya na mai fari cikin yadda wadannan matasa suka yi kasuwa, ganin yadda wasu kamfanonin gida suka zabi su ba wasunsu aiki.

Kwankwasiyya
Daliban Kwankwasiyya 370 a jirgin sama Hoto: www.solacebase.com
Asali: UGC

Za a ba matasan aiki a gida

Kamfanonin gidan da suka yi alkawarin daukar matasan aiki sun hada da Dangote group, BUA limited, jami'ar Skyline University, Tiamin Rice Mills da sauransu.

“Mun gamsu da muka ji 13 daga cikin mutane 370 da suka kammala digiri da matakin farko sun samu aiki a inda suka yi karatun digirinsu a Indiya.”
“Kuma an fara tunanin su fara karatun digir-digir (PhD).
“Don haka ina taya wadannan mutane 13 da dukkaninku murna game da nasarar ku, da kuma zama jakadun kwarai. Ina taya ku murnar dawowa lafiya.”

Kwankwaso ya dage a kan harkar ilmi

Kara karanta wannan

Ba ministan tsaro bane da AK-47: Ma'aikatar tsaro ta bayyana wa aka gani da AK-47

Tsohon gwamnan ya bayyana abin da ya sa ya dage wajen bunkasa harkar ilmin matasa a Kano. Da yake mulki, Kwankwaso ya tura mutane fiye da 2000 karatu.

Sanata Kwankwaso wanda ya yi gwamna sau biyu ya bayyana cewa zai cigaba da yin bakin kokarinsa domin ganin marasa karfi sun samu ilmi mai nagarta.

Matasa 370 sun amfana a Kano

Idan za ku tuna gidauniyar ta zakulo wadannan matasa ne bayan ta bada sanarwar za a tura ‘ya ‘yan marasa hali da suke da takardun digiri zuwa jami'o'in waje.

Wadannan matasa sun yi digiri a jami’o’i 14 da ke kasashen Amurka, nahiyar Asiya da birnin Dubai. Wasu kuma sun yi karatu ne a makarantun da ke Afrika.

Asali: Legit.ng

Online view pixel