VAT: Gwamnonin Arewa za su hada-kai da Gwamnatin Tarayya suyi shari’a da Jihohin Kudu

VAT: Gwamnonin Arewa za su hada-kai da Gwamnatin Tarayya suyi shari’a da Jihohin Kudu

  • Ana shari’a tsakanin wasu Gwamnonin Kudu da FIRS a kan batun harajin VAT
  • Gwamnonin Jihohin Arewa za su yi wa Jihohin Kudun tarin dangi a kotun koli
  • Akwai yiwuwar Zamfara da Kogi duk su shiga cikin wadanda suka daukaka kara

Abuja - Akwai alamu da ke nuna cewa gwamnatin tarayya da wasu gwamnonin jihohin Arewa za su kalubalanci hukuncin da kotu tayi a kan harajin VAT.

Babban lauyan gwamnati zai yi shari’a da gwamnatocin jihohin Legas, Ogun, Akwa Ibom da Oyo domin a warware gardama kan wanda zai rika karbar VAT.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa gwamnatin Ribas tana kalubalantar hukumar FIRS a kotun koli.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu jihohi na Arewa za su hada-kai da hukumar tattara haraji na kasa watau FIRS, su gwabza da gwamnatocin kudun a kotu.

Kara karanta wannan

2023: Ai ba a yin dole a siyasa – Tsohon Gwamnan Arewa ya yi wa Gwamnonin Kudu raddi

Babban lauyan gwamnatin jihar Kaduna, Chris Umar ya shaida wa Daily Trust cewa ba su kai ga cusa kansu a cikin shari’ar ba, amma akwai yiwuwar hakan.

Gwamnonin Najeriya
Gwamnoni tare da Buhari Hoto: www.tvcnews.tv
Asali: UGC

“Watakila kun ji matsayar kungiyar gwamnonin Arewa. Matsayar mu bai sha ban-bam da saura ba. Idan mun samu wani umarni akasin haka, za mu sanar.”

Gwamnoni uku sun hadu da AGF

Wata majiya ta bayyana wa Punch cewa gwamnonin Zamfara da Kogi za su yi wa Ribas taron dangi.

Ana tunanin gwamnoni uku na Arewacin Najeriya sun hadu da AGF a Abuja, a ranar Lahadi, 3 ga watan Oktoba, 2021, sun tattauna yadda za su shiga shari’ar.

“Gwamnonin za su bukaci a cusa su a cikin wadanda suka daukaka kara a kan hukuncin babban kotun tarayya wanda ya ba gwamnatin jihar Ribas gaskiya.”

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari za ta fara biyan daliban digiri da NCE kudin kashewa

Jihohin sun lura cewa idan FIRS ta sha kashi a kotun koli, za su rasa kudin da suke samu. Ana sa ran nan da ranar Talata, su hada takardun da za su kai kotu.

Siyasar cikin gidan PDP

Idan muka koma siyasar PDP, za mu je cewa takarar shugabancin PDP na iya zama tsakanin tsofaffin wasu Gwamnonin Arewa; David Mark da Ahmad Makarfi.

‘Ya ‘yan PDP suna so ne wanda bai taba canza sheka ba ya zama shugaban jam'iyya na kasa. Sanata David Mark da Sanata Ahmad Makarfi ba su taba barin PDP ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel