Jihar Niger: Mayaƙan Boko Haram sun ratsa mazaɓu 8 cikin 25, Shugaban Ƙaramar Hukuma

Jihar Niger: Mayaƙan Boko Haram sun ratsa mazaɓu 8 cikin 25, Shugaban Ƙaramar Hukuma

  • Shugaban karamar hukumar Shiroro a jihar Niger ya koka kan yadda 'yan Boko Haram ke shigowa yankinsa
  • Suleiman Chukuba ya ce yan Boko Haram din sun shiga a kalla mazabu guda 8 cikin 25 da ke karamar hukumar Shiroro
  • Chukuba ya ce gwamnati da jami'an tsaro na kokarin dakile matsalar amma ya nemi dauki daga gwamnatin tarayya

Niger - Mayakan Boko Haram sun mamaye garuruwa da dama a jihar Niger, inda suka raba wa mutane kudi suna daukansu a matsayin mayaka domin su taya su yaki da gwamnati, jami'in karamar hukuma da jiha ya shaidawa Reuters.

Suleiman Chukuba, shugaban karamar hukumar Shiroro na jihar Niger ya ce a halin yanzu mayakan Boko Haram suna mazabu 8 cikin jimillar 25 da ke karamar hukumarsa.

Read also

Adamawa: Magidanci mai 'ya'ya 3 ya rasa ransa bayan shan guba da ya yi sakamakon rikici da matarsa

Jihar Niger: Mayaƙan Boko Haram sun ratsa mazaɓu 8 cikin 25, Shugaban Ƙaramar Hukuma
Taswirar Jihar Niger. Hoto: Channels TV
Source: UGC

Chukuba ya ce:

"Ba a san adadin mayakan kungiyar Boko Haram da ke karamar hukumar Shiroro ba."

Boko Haram wacce ke yaki da karatun boko ta fara kai hare-hare ne tun 2009 sannan daga bisani kungiyar ISWAP da ta balle daga Boko Haram ita ma ta fara kai harin.

Yakin ya kashe kimanin mutum 350,000, miliyoyin mutane kuma sun rasa muhallinsu a cewar kididigar Majalisar Dinkin Duniya.

Yawan mutanen da ke Shiroro ya kai 331,000 a fadin kasa kilomita 4,7000 a cewar sashin gwamnatin jihar Niger.

Kwamishinan watsa labarai na jihar Niger Muhammad Sani Idris ya ce mayakan wadanda da farko ake zargin yan bindiga ne sun fara shigowa jihar. Amma Idris ya ce gwamnatin jihar da jami'an tsaro suna taka musu birki.

Read also

Ba na cikin matsananciyar bukatar takarar shugabancin kasa, Gwamnan Bauchi

Muna yin duk abin da ya kama a matsayin mu na jihar, in ji shi. Kuma zamu cigaba da hadin kai tare da jami'an tsaro da 'yan banga.

Rundunar sojojin Nigeria, a watan da ta gabata ta ce kimanin mayakan Boko Haram 6000 ne suka mika wuya.

Chukuba ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta turo karin sojoji yankin domin su yaki yan ta'addan.

Hotunan Mutane 5 Masu Garkuwa Da Mutane Da Ƙwararrun Mafarauta Suka Kama a Kogi

A wani labarin daban, kwararrun mafarauta a karamar hukumar Okehi a jihar Kogi sun yi nasarar kama mutane biyar 'yan kungiyar masu garkuwa da mutane, LIB ta ruwaito.

An kama mutane biyar din da ake zargi a safiyar ranar Talata a Atami, wani gari da ke wajen Osara a ranar Talata, 27 ga watan Satumban shekarar 2021.

King Habib, babban hadimi ga shugaban karamar hukumar Okehi a bangaren watsa labarai, Hon Abdulraheem Ohiare Ozovehe ya tabbatar da kama wadanda ake zargin, yana mai cewa tawagar sun dade suna adabar mutane a titin Okene-Lokoja da Okene-Auchi a jihar Kogi State.

Read also

Da Duminsa: Mutane Sun Shiga Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Hallaka Mutum 3 a Awka

Source: Legit

Online view pixel