Abinda yasa muke kai yara karatu kasashen ketare, Kwankwasiyya

Abinda yasa muke kai yara karatu kasashen ketare, Kwankwasiyya

- Gidauniyar cigaba da Kwankwasiyya ta ce tana tura dalibai kasashen ketare ne don su samu gogewa

- A cewar shugaban gidauniyar, samun gogewa a kasashen ketare zai sa daliban su iya gogayya da sa'o'insu a duniya

- Sanata Kwankwaso yayi wannan jawabin ne a ranakun karshen mako inda yace tuni wadanda suka dawo sun fara samun aiki

Gidauniyar cigaba ta Kwankwasiyya (KDF) ta yi bayanin cewa ta tura a mutum 370 karatun digiri na biyu da na uku a jami'o'in kasashen ketare don ta basu damar samun gogayya a duniya.

Shugaban gidauniyar kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana hakan a cikin ranakun karshen mako a wani taro da yayi da sabbin dawowa daga karatu a kasashen ketare.

Ya ce abinda yasa suke zabar jami'o'in ketare shine bai wa daliban damar gogewa ta yadda za su iya fito na fito da sa'o'insu a duniya, Daily Trust ta wallafa.

KU KARANTA: Kano: 'Yan Hisbah sun damke matasa 2 akan zargin tura wa matar aure bidiyon shahanci

Abinda yasa muke kai yara karatu kasashen ketare, Kwankwasiyya
Abinda yasa muke kai yara karatu kasashen ketare, Kwankwasiyya. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

"Abun farin ciki ne ta yadda 13 daga cikin 370 na daliban da suka gama da digiri mai darajar farko sun samu aiki a makarantun da suka gama a India kuma za su cigaba da karatu," yace.

KU KARANTA: Da duminsa: Sojoji sun mamaye Dikwa, sun fatattaki mayakan Boko Haram

A wani labari na daban, ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya ce akwai shirin cewa 'yan ta'adda za su iya sace wasu jama'an domin su tozarta gwamnatin tarayya.

Ministan ya sanar da hakan ne a ranar Litinin bayan ganawa da yayi da shugaban kasa Muuhammadu Buhari, The Cable ta wallafa.

Tun a farko ministan ya mika alkawarin shugaban kasa Muhammadu Buhari inda yace sace yaran makarantar sakandare na Jangebe zai zama na karshe a kasar nan.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel