Ba ministan tsaro bane da AK-47: Ma'aikatar tsaro ta bayyana wa aka gani da AK-47

Ba ministan tsaro bane da AK-47: Ma'aikatar tsaro ta bayyana wa aka gani da AK-47

  • An yada jita-jitar cewa, an ga ministan tsaro a Najeriya dauke da bindiga AK-47 yayin shiga mota
  • Rahotanni da muke samu daga majiyoyi sun bayyana cewa, ba ministan bane, sannan ba ma irin motarsa ba kenan
  • Hujjoji sun bayyana cewa, mutumin da ke dauke da bindigar wani shugaban makarantar sojoji ce da ke jihar Benue

Ma'aikatar tsaro ta musanta ikirarin da ake yadawa cewa mutumin da ke dauke da bindigar AK47 a bidiyon da ya bazu a kafafen sada zumunta shi ne minista Bashir Magashi.

Mai taimaka wa Magashi na musamman kan harkokin yada labarai, Mohammad Abdulkadri, a cikin wata sanarwa, ya bayyana cewa wanda aka gani a bidiyon shugaban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Muhalli ta Sojin Najeriya (NACEST) ne da ke Makurdi, jihar Neja.

Kara karanta wannan

Adamawa: Magidanci mai 'ya'ya 3 ya rasa ransa bayan shan guba da ya yi sakamakon rikici da matarsa

Ya musanta batun ne a jiya Lahadi 3 ga watan Oktoba, inda ya bayyana cewa lallai ba mai gidansa bane.

Abdulkadri ya yi bayanin cewa duba da yanayin ofis dinsa, shugaban na NACEST yana da ikon doka na daukar makami na doka lokacin tafiya, The Nation ta ruwaito.

Ba ministan tsaro bane da AK-47: Ma'aikatar tsaro ta bayyana wa aka gani da AK-47
Ministan tsaron Najeriya, Bashir Magashi | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Mai taimaka wa ministan ya kafa hujja kan ikirarinsa ta hanyar lura da cewa launin kore na Soja a jikin mota kirar Innonson Jeep da kuma alamar NACEST a jikin motar jami'in isassun shaidu ne cewa mutumin ba Magashi bane, Leadership ta kara da cewa.

Ya kara da cewa ministan, kamar takwarorinsa na sauran ma’aikatu, yana amfani da bakar mota ne kirar Land Cruiser jeep.

A kalamansa:

"A zahiri, launin kore na soja a jikin mota Innonson Jeep da sitirar NACEST a jikin motar hukuma cikakkun isassun hujjoji ne na kawar da ikrarin faifan bidiyon da ake magana akan shi a matsayin Babban Ministan Tsaro wanda ke amfani da bakar mota kirar Land Cruiser Jeep kamar takwarorinsa na sauran ma'aikatu."

Kara karanta wannan

Ba na cikin matsananciyar bukatar takarar shugabancin kasa, Gwamnan Bauchi

COAS ga sojoji: Kada ku daga kafa wajen ragargazar 'yan ta'adda

A wani labarin, Babban hafsan sojin kasa Laftanar Janar Farouk Yahaya ya umarci runduna ta bataliya ta 4 ta musamman da ke Doma da su ci gaba da jajircewa don ganin sun kubutar da kasar daga hannun mayakan Boko Haram da sauran 'yan ta'adda a Arewa da sauran sassan kasar.

Yahaya ya ba da wannan umarnin ne a lokacin da yake zantawa da Daily Trust yayin ziyarar aiki da ya kai hedikwatar bataliyar da ke karamar Hukumar Doma ta Jihar Nasarawa don duba wasu wurare a barikin.

Ya ce kalubalen tsaro da ke fuskantar kasar nan ba za a iya shawo kansu ba idan aka babu kulawa da jajircewa daga gwamnatin tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.