Gwamnan Arewa ya yi iƙirarin wasu manya sun daƙo hayar masu kisa daga ƙasar waje su kashe shi
- Samuel Ortom, gwamnan jihar Benue ya yi ikirarin akwai wasu manyan mutane da ke barazanar kashe shi
- Gwamna Ortom a ranar Lahadi, 3 ga watan Oktoba, ya yi ikirarin cewa an dauko hayar wasu daga Sudan su kashe shi
- Amma, Gwamnan ya ce babu damuwa idan ya rasa ransa a yayin hidimtawa mutanen jiharsa
Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue, a ranar Lahadi 3 ga watan Oktoba ya yi ikirarin cewa wasu mutane na kitsa yadda za su kashe shi.
Ortom, ya yi wannan zargin ne a cibiyar masu zuwa hajji na kirista ta Sesugh Maria da ke karamar hukumar Gwer na jihar Benue kamar yadda AIT News ta ruwaito.
Gwamnan na Benue ya kuma yi ikirarin wadanda ke son kashe shi sun dauko hayar makasa daga Sudan don su kai masa hari.
Sai dai, Ortom ya ce ya yanke shawarar zai cigaba da yi wa mutanensa hidima idan kuma ya mutu yayin hakan toh haka Allah ya so.
Ya ce:
"Babu ja da baya a kan wannan lamarin. Babu damuwa, Idan na mutu, shi kenan. Duk da barazanar da ake min, idan na mutu, na mutu. Tamkar Shedrack, Mishack da Abednego na ke.
"A makon da ta gabata an fada min cewa an dakko hayan wasu makasa daga Sudan domin su kashe ni ..."
"Zan cigaba da yi wa mutane na hidima. Na mayar da hankali wurin aikin domin su suka zabe ni domin in aiwatar da abubuwan da suke so. Babu wanda zai firgita ni ko yasa in dena abin da na ke yi har sai an yi wa mutane na adalci a jihar Benue."
Borno: An tafka ƙazamin faɗa tsakanin Boko Haram da ISWAP, an kashe 24
A wani labarin daban, 'yan ta'addan Boko Haram sun kashe mayakan Islamic State of West Africa Province, ISWAP guda 24 a duwatsun Mandra da Gaba a yankin Gwoza a ranar Juma'a.
Lamarin ya faru ne a yayin da yan Boko Haram din karkashin wani kwamanda Aliyu Ngulde, suka yi musayar wuta da mayakan ISWAP karkashin jagoracin wani Abou Aseeya a yankin mai duwatsu.
A cewar wasu majiyoyi da suka yi magana da PRNigeria, rikicin tsakanin kungiyoyin biyu na ramuwayar gayya ne sakamakon harin da 'yan ISWAP suka rika kai wa yan Boko Haram a baya-bayan nan.
Asali: Legit.ng