Kungiyar Miyetti Allah tayi kaca-kaca da Sarakuna, Gwamnonin da suka yi taro a Kaduna

Kungiyar Miyetti Allah tayi kaca-kaca da Sarakuna, Gwamnonin da suka yi taro a Kaduna

  • Miyetti Allah Kautal Hore ta soki zaman da shugabannin Arewa suka yi a Kaduna
  • Kungiyar tace Gwamnoni da Sarakuna ba su damu da halin da Fulani suke ciki ba
  • Shugaban Miyetti Allah Kautal Hore yace ana wulakanta Makiyaya a jihohin Kudu

Bauchi - Miyetti Allah Kautal Hore ta reshen jihar Bauchi ta yi tir da kungiyar gwmnonin Arewa, ta zarge ta da rashin damu wa da halin kabilar Fulani.

Miyetti Allah Kautal Hore tayi magana ne a kan taron da gwamnoni da sarakuna Arewa suka yi, suka ce ba a tabo cin kashin da ake yi wa makiyaya ba.

Jaridar Punch ta rahoto kungiyar makiyayan tana cewa ana wulakanta makiyaya Fulani da suke kiwon dabbobinsu musamman a yankin kudancin kasar.

Shugaban kungiyar, Muhammad Hussaini, ya yi mamakin yadda gwamnonin suka ki tattauna wa a kan wulakancin da ake yi wa makiyaya a jihohin kudu.

Read also

Gwamnan Arewa ya yi iƙirarin wasu manya sun daƙo hayar masu kisa daga ƙasar waje su kashe shi

Muhammad Hussaini yace bai kamata shugabannin wanda sune wakilan al’umma, su yi taro su tashi, ba tare da an yi maganar abin da ya shafi Fulani ba.

Gwamnonin Arewa
Gwamnonin Arewa Hoto: Facebook /NGF
Source: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, ana wulakanta makiyaya, har a kashe wasu yayin da suke neman abincin dabbobinsu.

Hussaini yace an takaita yawon da makiyaya za su iya yi a Najeriya, duk da cewa tsarin mulki ya ba kowa dama ya taka kafarsa zuwa duk inda ya ga dama.

Shugaban kungiyar ya yi wannan jawabi a Bauchi, a ranar Laraba, 29 ga watan Satumba, 2021, yace batun ran al’umma ya fi inda za a kai mulki muhimmanci.

Aljihunsu suke kare wa

“A maimakon gwamnonin Arewa su nuna damuwa kan abin da gwamnonin kudu suke yi wa makiyaya, sai suka buge da maganar rama abin da aka yi masu.”
“Sun zauna sun tattauna abin da ya shafe su, yadda za su azurta kansu. A dalilin wannan, mun yi tir da gwamnonin Arewa da Sarakuna da suka halarci taron.”

Read also

Gwamnonin kudu maso kudu sun shiga ganawar gaggawa a jihar Ribas

Kungiyoyin Arewa sun yi magana

‘Yan Arewa suna rigima a kan inda Shugaban Najeriya zai fito a 2023. Kungiyar MNF ta ko dai mulki ya koma Kudu a 2023, ko ya fada hannun ‘Dan Arewa ta tsakiya.

Kungiyar NEF ta yabi matsayar da shugabanni da gwamnonin Arewa suka dauka a Kaduna. Akasin haka kuma, kungiyar MNF ta nuna adawarta ga wannan batu.

Source: Legit

Online view pixel