2023: Wanda zai zama Magajin Shugaba Buhari ya raba kan manyan Kungiyoyin 'Yan Arewa

2023: Wanda zai zama Magajin Shugaba Buhari ya raba kan manyan Kungiyoyin 'Yan Arewa

  • Kan Northern Elders Forum da Middle Belt Forum ya rabu a game da zaben 2023
  • NEF ta yabi matsayar da shugabanni da gwamnonin Arewa suka dauka a Kaduna
  • Kungiyar MNF tace ko mulki ya je Kudu, ko kuma a tsaida ‘Dan Arewa ta tsakiya

Nigeria - Kungiyoyin Northern Elders Forum da Middle Belt Forum sun samu sabani a kan bangaren da sabon shugaban Najeriya zai fito a zaben 2023.

Jaridar Daily Trust tace NEF da MNF sun yarda cewa dokar kasa da tsarin mulki ba su san da zaman tsarin karba-karba da jam’iyyu suka bijiro da shi ba.

Amma duk da haka, kungiyar Middle Belt Forum ta mutanen Arewa maso tsakiya sun ce za su goyi bayan Kudu ko yankin Arewa ta tsakiya ne kurum a 2023.

Read also

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa na lalata, aure ya mutu a daren farko

Ita kuma kungiyar NEF ta dattawan Arewacin Najeriya ta yabi matsayar da gwamnonin jihohin Arewa da sarakunan yankin suka dauka a farkon makon nan.

Da suka yi wani zama a garin Kaduna, gwamnoni da masu sarautar gargajiya na Arewa sun yi wa shugabannin kudu raddi game da batun fito da shugaban kasa.

Hakeem Baba-Ahmed ya yaba

Jaridar ta kawo rahoto cewa darektan yada labarai da wayar da kai na NEF, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya ji dadin martanin da manyan Arewa suka ba na Kudu.

Shugaba Buhari
Buhari yana kamfe a Kaduna Hoto: www.sunnewsonline.com
Source: UGC

Hakeem Baba-Ahmed yake cewa shugabannin yankin Arewa da a baya suke jin kunyan bude bakinsu, su maida wa gwamnonin kudu raddi, sun yi abin a yaba.

“Akwai dokar da tayi bayanin yadda za a zabi shugaban kasa, wannan ne matsayarmu. Mun ji dadi da gwamnoni 19 suka dauki matsayar da muke kai tuni.”

Read also

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Baba-Ahmed yace matsayar da shugabannin yankin suka dauka, shi ne ra’ayin NEF tun ba yau ba.

Arewa dabam, tsakiyar Najeriya dabam?

Shugaban kungiyar MBF, Dr. Pogu Bitrus yace Arewa fa ba a dunkule ta ke ba, ya kuma ce sai dai mulki ya rika yawo tsakanin Arewa, kudu da tsakiyar Najeriya.

Bitrus yake cewa suna kira mulki ya je Arewa maso tsakiya a 2023. Kungiyar MBF tace kasar nan za ta auka wa rikici idan aka ce dole mulki ya tsaya a inda yake.

Ohanaeze ta ja kunnen PDP

A jiya ne a aka ji kungiyar Ohanaeze mai kare hakkin Ibo, tayi wa Gwamnonin Arewa raddi, tace yankin bai amfana da duk shugabannin da bangaren ya fitar ba.

Ohanaeze Ndigbo tace tun 1998 shugabannin Kudu da Arewa suka yarda mulki zai rika yawo. A dalilin haka kungiyar ta ja-kunnen PDP kan kai takara zuwa Kudu.

Read also

Ohanaeze: Jam’iyyar PDP ta mutu murus idan tayi kuskure tsaida ‘Dan Arewa a zaben 2023

Source: Legit

Online view pixel