Gwamnonin kudu maso kudu sun shiga ganawar gaggawa a jihar Ribas

Gwamnonin kudu maso kudu sun shiga ganawar gaggawa a jihar Ribas

  • Rahotanni da muke samu sun bayyana cewa, gwamnonin kudu maso kudu sun shiga taron gaggawa
  • Taron nasu na zuwa bayan da gwamnonin Arewa suka zauna don tattauna batutuwa da suka shafi harajin VAT
  • Ana kyautata zaton su din za su zauna kan wannan batu, duk da cewa basu bayyana makasudin taron ba

Ribas - A halin yanzu gwamnonin jihohi shida na shiyyar siyasar yankin Kudu-maso-Kudu suna taro a gidan gwamnatin jihar Ribas da ke Fatakwal.

Ko da yake ba a san dalilin taron ba tukuna, wakilin Punch ya ba da rahoton cewa lamuran harajin VAT da Shugabancin Kudanci a 2023 na daga cikin abubuwan da za su caccaka tsinke a tattaunawar.

Yanzu-Yanzu: Gwamnonin kudu maso kudu za su yi ganawar gaggawa a jihar Ribas
Taron gwamnonin kudu maso kudu | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Twitter

An ga gwamna mai masaukin baki, Nyesom Wike, da Gwamna Godwin Obaseki na Edo, suna ta hira a wurin taron.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: IGP ya tura sabon kwamishina da dakaru na musamman

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Kudu-maso-Kudu, Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta, da takwaransa na Jihar Edo, Gwamna Godwin Obaseki, na cikin wadanda suka halarci taron.

Sun isa da misalin karfe 10:30 na safe sannan daga baya gwamnonin jihar Bayelsa, Douye Diri, da takwaransa na jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel suka iso.

A lokacin wannan rahoto, har yanzu gwamnan jihar Kuros Riba, Ben Ayade, bai iso wurin taron ba, inji rahoton Channels Tv.

Taron yana gudana ne wata daya kafin taron Kungiyar Gwamnonin Kudu, wanda kuma aka shirya za a yi a Fatakwal.

Sauya sheka: Gwamna Buni ya karbi mambobin majalisar jihar Anambra 11 zuwa APC

A wani labarin daban, Gwamnan jihar Yobe, kuma shugaban kwamitin tsare-tsaren babban taron jam'iyyar APC na rikon kwarya, Mai Mala Buni ya karbi wasu jiga-jigan siyasar jihar Anambra daga wasu jam'iyyu zuwa APC.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC za ta yaki satar kudin fanshon ma’aikata, wasu mutane sun wawuri N150bn

Ana ci gaba da yawaita sauya sheka a cikin wannan shekara, lamarin da ya kawo cece-kuce a jam'iyyun siyasa daban-daban na Najeriya.

Legit.ng Hausa ta lura cewa, akalla 'yan majalisa daga jihar Anambra 11 suka sauya sheka zuwa APC wanda gwamnan ya karbe su cikin lumana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.