Dan kasuwa ya kama matarsa da abokinsa a gado, ya ce ya biya N893k ta zama ta shi

Dan kasuwa ya kama matarsa da abokinsa a gado, ya ce ya biya N893k ta zama ta shi

  • Bidiyon dan kasuwa ya kama matarsa ta na cin amanarsa da abokinsa ya bazu kuma ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta
  • Dan kasuwan mai suna Issa Kasili ya kama abokinsa Mayombi Mwela da matarsa a wani masaukin baki da ke Tanzania
  • Fusataccen dan kasuwan ya sanar da Mayombi cewa ya bar masa matar amma ya bukaci a biya shi KSh 240,000 (N893,799)

Tanzania - Me za ka yi idan ka kama masoyiyar ka da abokan ka a gado suna cin amanar ka? Toh, wani dan kasar Tanzania ya kama matarsa da abokinsa suna cin amanarsa kuma ya bukaci wasu kudade.

Dan kasuwa ya kama matarsa da abokinsa a gado, ya ce ya biya N893k ta zama ta shi
Dan kasuwa ya kama matarsa da abokinsa a gado, ya ce ya biya N893k ta zama ta shi. Hoto daga Muro TV
Source: UGC

Kamar yadda EA TV ta wallafa, Issa Kasili, dan kasuwan kasar Tanzania daga Mpimbwe, ya kama matarsa da abokinsa mai suna Mayombi Mwela suna cin amanarsa.

Read also

Gwamnan Arewa ya yi iƙirarin wasu manya sun daƙo hayar masu kisa daga ƙasar waje su kashe shi

Ya kama su biyun a otal kuma daga nan ya bukaci a biya shi KSh 240,000 (N893,799).

A wani bidiyo, an ga Kasili ya tsare su biyun a wani masaukin baki kuma bidiyon ya bazu a kafar sada zumuntar zamani.

An ji fusataccen Kasili na daka tsawa tare da masifa ga Mayombi kan cin amana.

"Ka kwanta da mata ta Mayombi, ka cika babban burin ka."

Kasili ya kara da cewa da daya dama gare shi da matar kafin ya ce a lokacin ba ya kaunar ta.

Sai ka biya ni wasu kudi, Kasili ya mika bukata

"Kin haifar min da daya kuma yanzu kina tunanin ba za ki tabu ba. Aurenmu a yau ya zo karshe," yace.

Daga nan Kasili ya sanar da Mayombi cewa ya tafi da matarsa kuma ya bar masa kafin ya bukaci a biya shi wasu kudi.

Read also

Ba ministan tsaro bane da AK-47: Ma'aikatar tsaro ta bayyana wa aka gani da AK-47

"Ka biya ni dukkan abinda na kashe sannan ka tafi da ita. Yanzu ta zama matar ta," yace

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, Mayombi a take ya biya Kasili kudin da ya bukata.

Sojin sama sun sheke mutum 28 da ke kai wa 'yan ISWAP kayan bukata a Kukawa

A wani labari na daban, a kalla 'yan ta'adda 28 da ke da alaka da Islamic State of the West African Province (ISWAP) tare da masu basu hadin kai a kasuwancin kifi ne suka hadu da ajalinsu a ranar Lahadi, PRNigeria ta tattaro hakan daga majiyoyin sirri.

Majiyoyin da aka tura yankin arewa maso gabas a jihar Borno, sun ce mayakan da masu basu hadin kai da suka hada da masunta an kashe su ne sakamakon shiryayyen harin dakarun kasa da na sama wanda sojin suka hada a Daban Masara da ke karamar hukumar Kukawa ta jihar.

Read also

Lars Vilks: Mutumin da ya yi zanen ɓatancin Annabi Muhammadu a Sweden ya mutu a hatsarin mota

PRNigeria ta tattaro cewa, bayan bayanan sirrin da aka samu har aka kai farmakin, an yi nasarar sheke miyagu ashirin da ke taimaka wa 'yan ta'addan da kayayyakin bukata.

Source: Legit

Online view pixel