'Yan bindiga sun kashe mutum 30 yayin harin da suka kai ƙauyen jihar Niger

'Yan bindiga sun kashe mutum 30 yayin harin da suka kai ƙauyen jihar Niger

  • Ƴan bindiga sun afka ƙauyen Sarkin Pawa da ke jihar Niger sun halaka kimanin mutum 30
  • Kwamishinan ƴan sandan jihar Niger, Monday Bala Kuryas ya tabbatar da afkuwar lamarin
  • Kuryas ya ce an tura ƙarin jami'ai zuwa yankin don bawa mutane kariya sannan an fara bincike don gano wadanda ke da hannu

Jihar Niger - A kalla mutane 30 ne ƴan bindiga suka kashe a ƙauyen Kachiwe, Sarkin Pawa da ke ƙaramar hukumar Munya da ke Jihar Niger.

SaharaReporters ta ruwaito cewa ƴan bindigan daga maɓuyarsu da ke dajin Birnin Gwari a jihar Kaduna sun kai hari ƙauyen da wasu da ke kewayensa.

Mutane sun shiga ruɗani yayin da ƴan bindiga suka kashe mutum 30 a Niger
Taswirar Jihar Niger. Hoto: Channels TV
Source: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Read also

Abun mamaki: Bidiyo da hotunan yadda Firayim ministan Ethiopia ya koma 'direban' Buhari

Ahmed Ibrahim Matana, Sakataren gwamnatin Jihar Niger, ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Ya bukaci mutanen gari su rika taimakawa jami'an tsaro da bayanai masu amfani da zai taimaka musu maganin yan bindiga da masu garkuwa.

Monday Bala Kuryas, Kwamishinan yan sandan jihar ya ce tuni dai an fara bincike a kan afkuwar lamarin.

Ya ce:

"An tura tawagar ƴan sanda zuwa yankin domin tsare lafiya da duniyoyin al'umman Sarkin Pawa. Ana ƙoƙarin gano wadanda ke da hannu a mummunan laifin."

Ya bayyana cewa, a baya, an kashe mutane uku yayin wani harin mai kama da wannan a ƙaramar hukumar Kagara na jihar.

Hotunan Mutane 5 Masu Garkuwa Da Mutane Da Ƙwararrun Mafarauta Suka Kama a Kogi

A wani labarin daban, kwararrun mafarauta a karamar hukumar Okehi a jihar Kogi sun yi nasarar kama mutane biyar 'yan kungiyar masu garkuwa da mutane, LIB ta ruwaito.

An kama mutane biyar din da ake zargi a safiyar ranar Talata a Atami, wani gari da ke wajen Osara a ranar Talata, 27 ga watan Satumban shekarar 2021.

Read also

Ganduje, Amaechi, Ikweremadu, wasu mutum 22 da suke cin taliyar siyasa tun 1999 har yanzu

King Habib, babban hadimi ga shugaban karamar hukumar Okehi a bangaren watsa labarai, Hon Abdulraheem Ohiare Ozovehe ya tabbatar da kama wadanda ake zargin, yana mai cewa tawagar sun dade suna adabar mutane a titin Okene-Lokoja da Okene-Auchi a jihar Kogi State.

Source: Legit

Online view pixel