Ganduje, Amaechi, Ikweremadu, wasu mutum 22 da suke cin taliyar siyasa tun 1999 har yanzu
- Akwai ‘yan siyasar da tun 1999 suke rike da mukaman gwamnati har yau
- Wadannan ‘yan siyasan suna ta canza ofis ne na tsawon shekara 22 a jere
- Daga cikinsu akwai Ahmad Lawan, Abdullahi Ganduje, da Ali Modu Sheriff
Nigeria - Shekara 22 kenan akwai wasu ‘yan siyasa 22 a kasar nan da har yanzu suna cikin gwamnati. An cigaba da dama wa da wadannan mutane tun 1999.
Jaridar Daily Trust tayi wani bincike na musamman, ta tattaro ‘yan siyasar da har gobe ake yi da su. Tun da aka dawo mulkin farar hula dai suke rike da mukamai.
Ga ‘yan siyasar nan kamar yadda jaridar ta kawo:
1. Ahmad Lawan
A 1999 ya zama ‘dan majalisar wakilan tarayya, a 2007 aka zabe shi a matsayin Sanatan Yobe ta Arewa. Shugaban majalisar dattawa tun 2019 zuwa yanzu.
2. Danjuma Goje
Mohammed Danjuma Goje ya zama Minista a 1999, tsakanin 2003 da 2011 ya yi gwamnan jihar Gombe. Tun bayan nan ne yake Sanata a majalisar dattawa.
3. Ike Ekweremadu
Sanata Ike Ekweremadu ya shiga gwamnati tun 1997, ya rike mukamai a gwamnatin Enugu daga 1999 zuwa 2001. A 2003 ya zama Sanata, har yau yana nan.
4. Raji Fashola
Babatunde Raji Fashola yana cikin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a 1999. A 2007 ya zama gwamnan Legas. Tun bayan nan kuma yake Minista har yau.
5. Adamu Aliero
Muhammad Adamu Aliero ya yi gwamnan Kebbi daga 1999. A 2007 ya bar Minista, ya zama Ministan Abuja. Yanzu haka ya sake koma wa majalisar dattawa.
6. Aliyu Wamakko
Tsohon mataimakin gwamna, tsohon gwamna, yanzu Sanata mai wakiltar Sokoto ta yamma.
7. Rauf Aregbesola
Kwamishina a gwamnatin Tinubu, zuwa gwamnan Osun har 2018, yanzu yana Ministan gida.
8. Chris Ngige
Tsohon Sakataren PDP, Gwamnan Anambra a 2003, tsohon Sanata, kuma Ministan kwadago.
9. George Akume
Akume ya yi gwamna daga 1999 zuwa 2007, sai ya zama Sanata har 2019, yanzu yana Minista.
10. Rotimi Amaechi
Amaechi ya yi shugaban majalisar Ribas daga 1999, sai ya zama Gwamna, daga nan yake Minista.
Sauran ‘yan siyasar sune:
11. Enyinnaya Abaribe
12. James Manager
13. Abdullahi Umar Ganduje
14. Pauline Tallen
15. Ali Modu Sheriff
Sun yi Gwamna, yanzu suna Majalisa
Ragowar sune wadanda sun yi gwamna, yanzu suna majalisar dattawa
16. Rochas Okorocha
17. Abdullahi Adamu
18. Ibikunle Amosun
19. Orji Uzor Kalu
20. Sam Egwu
21. Ibrahim Geidam
22. Gabriel Suswam
Lissafin PDP a 2023
A makon da ya wuce ne kuka ji cewa ana tunani jam’iyyar adawa ta PDP tana shirin watsi da ‘Yan siyasan Arewa a takarar Shugaban kasan da za ayi a shekarar 2023.
Idan aka tafi a haka, babu mamaki ‘Dan Kudu zai rike wa PDP tuta a zaben 2023. A halin yanzu an ba 'Dan Arewa dama ya fito takarar kujerar shugaban jam'iyyar PDP.
Asali: Legit.ng