Katsina: Ƴan Sanda Sun Kama Ƴan Ta'adda 2, Sun Ceto Mutum 10 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Katsina: Ƴan Sanda Sun Kama Ƴan Ta'adda 2, Sun Ceto Mutum 10 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce ta kama mutane 2 da ake zargin ‘yan ta’adda ne
  • Har ila yau ta samu nasarar ceto mutane 10 da masu garkuwa da mutane su ka sace
  • Kakakin rundunar, SP Gambo Isah ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Talata a Katsina

Katsina - Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta bayyana yadda ta kama mutane 2 da ake zargin ‘yan bindiga ne kuma ta ceto mutane 10 daga masu garkuwa da mutane.

Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, kakakin rundunar, SP Gambo Isah, ya bayyana hakan a wata takarda da ya ba manema labarai ranar Talata a Katsina.

Katsina: Ƴan Sanda Sun Kama Ƴan Ta'adda 2, Sun Ceto Mutum 10 Da Aka Yi Garkuwa Da Su
'Yan Sanda Sun Kama Ƴan Ta'adda 2, Sun Ceto Mutum 10 Da Aka Yi Garkuwa Da Su a Katsina. Hoto: Daily Nigerian
Source: Facebook

Isah ya bayyana yadda ‘yan sanda su ka yi musayar wuta da ‘yan bindiga

Read also

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa na lalata, aure ya mutu a daren farko

A cewar kakakin:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“A ranar 20 ga watan Satumban 2021, rundunar ta samu nasarar kama wani matashi mai shekaru 30 daga Sabon Garin Faguwa karkashin karamar hukumar Dutsinma wanda ya koma zama a daji.
“Shu’umin dan bindigan yana karkashin Sani Muhidinge ne, wanda yanzu haka ‘yan sanda suke nema ido ruwa a jallo.
“Sannan sun kama wani takadarin dan bindiga mai shekaru 22 dan Mai Gezoji, Tashar Mai Alawa dake karkashin karamar hukumar Danmusa.
“Tushen lamarin shine yadda ranar 15 ga watan Satumban 2021 ‘yan bindiga suka shiga kauyen Kitibawa dake karamar hukumar Dutsinma da kafa su na harbe-harbe.
“Sakamakon harbin sun hallaka ‘yan kauyen guda 2, sun banka wa shaguna wuta sannan suka sace mata 18 da jarirai 7.
“Bayan samun wannan labarin ne kwamandan ‘yan sanda na Dustinna, ACP Aminu Umar, ya jagoranci rundunar sa suka dakatar da ‘yan bindigan su ka fara musayar wuta.

Read also

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

“Sakamakon jajircewar ‘yan sandan da jarumtar su ya sa ‘yan bindigan su ka ji aman wuta su ka tsere daji da raunuka da dama.
“Bayan mayar da harin ne ‘yan sanda su ka ceto mata 2, tumaki 60, shanu 34 da jaki daya.”

Kamar yadda Isah ya shaida, binciken sirri da su ka gudanar ya sa a ranar 20 ga watan Satumba su ka kamo wani mutum mai shekaru 45 dan Tashar Mai Alawa dake karamar hukumar Danmusa da ake zargin ya na bai wa ‘yan bindiga labaran sirri kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Sannan sun kara kama wani mutum mai shekaru 34 wanda ma’aikacin asibiti ne, inda yake yi wa ‘yan bindiga aiki.

Sarkin Katsina ya barranta da matsayar Sheikh Gumi: Kisa ya dace da ƴan bindiga ba tattaunawa da su ba

A wani labarin daba, mai martaba Sarkin Katsina ya ce tunda ƴan bindiga sun zaɓi su rika kashe mutane 'suma bai dace a bar su da rai ba'.

Read also

NDDC Ta Zama Saniyar Tatsa Ga ’Yan Siyasa, In Ji Gwamna Wike

Sarkin na Katsina, Abdulmuminu Usman ya ce ba abin da ya dace da ƴan bindigan da ke kashe mutane a arewa maso yamma illa kisa.

Sarkin ya yi wannan furucin ne yayin taron tsaro na masu ruwa da tsaki a ranar Talata a Katsina kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Source: Legit

Online view pixel