Sarkin Katsina ya barranta da matsayar Sheikh Gumi: Kisa ya dace da ƴan bindiga ba tattaunawa da su ba

Sarkin Katsina ya barranta da matsayar Sheikh Gumi: Kisa ya dace da ƴan bindiga ba tattaunawa da su ba

  • Sarkin Katsina Abdulmuminu Usman ya ce kisa ne ya dace da ƴan bindigan da ke adabar arewa maso yamma
  • Sarkin ya ce baya goyon bayan tattaunawa da su ko afuwa tunda sun zaɓi su rika kashe mutane babu dalili
  • Abdulmuminu Usman ya kuma shawarci gwamnatoci a dukkan matakai su gaggauta hukunta ƴan bindigan don zama darasi ga wasu

Jihar Katsina - Mai martaba Sarkin Katsina ya ce tunda ƴan bindiga sun zaɓi su rika kashe mutane 'suma bai dace a bar su da rai ba'.

Sarkin na Katsina, Abdulmuminu Usman ya ce ba abin da ya dace da ƴan bindigan da ke kashe mutane a arewa maso yamma illa kisa.

Sarkin Katsina: Kisa ya dace da ƴan bindiga ba tattaunawa da su ba
Mai Martaba Sarkin Katsina, Abdulmuminu Usman. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Kada ku tausayawa yan bindiga, ku buɗe musu wuta koda sun shiga cikin mutane, Gwamnan Arewa ya hasala

Sarkin ya yi wannan furucin ne yayin taron tsaro na masu ruwa da tsaki a ranar Talata a Katsina kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Wadanda suka hallarci taron sun hada da Gwamna Aminu Masari, Ministan Labarai da Al'adu, Lai Mohammed, Sarkin Daura, Umar Faruk Umar da wasu da dama.

Sarkin ya ce tunda ƴan bindigan sun yanke hukuncin su rika kashe mutane suma bai dace a bar su da rai ba, rahoton Premium Times.

Sarkin Katsina ya koka kan jinkirin hukunta ƴan bindiga

Sarkin ya kuma koka kan yadda ake jinkiri wurin hukunta ƴan bindiga yana mai cewa 'hakan baya zama gargadi ga wasu ɓata garin'

A cewar Sarkin, ya kamata gwamnati a dukkan matakai su tashi tsaye don ganin an hukunta yan bindiga yana mai cewa bai dace mutum ya zama ɗan fashi ba da sunan nuna rashin jin dadin sa.

Kara karanta wannan

Sojoji sun hallaka kasurguman yan bindiga 5, tare da mabiyansu 23 a Zamfara

Yan bindigan dai sun addabi mutane a yankunan arewa maso yamma, suna garkuwa da mutane suna karbar kudi tare da kisa da ƙone-ƙone.

Wasu gwamnonin jihohin kamar Katsina, Zamfara, Sokoto sun dauki matakan toshe layukan waya, hana sayar da fetur a jarka, hana cin wasu kasuwanni don daƙile ƴan bindigan.

Sarkin ya kuma soki mutane irin su Sheik Ahmad Gumi da ke kira ga gwamnatoci su tattauna da 'yan bindiga har ma su duba yiwuwar yi musu afuwa da basu tallafi.

Masari: Muna cin nasara kan 'yan bindiga, sojoji na gasa musu aya a hannu

A wani labarin daban, Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya ce sababbin salon yaki da ta’addancin da gwamnati ta bullo da su a jihar Katsina su na aiki kuma ana samun nasarori kwarai wurin yaki da ta’addanci.

Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wani taro wanda suka yi da ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed akan matsalar tsaron a jihar.

Kara karanta wannan

Kaduna: Hotunan 'yan sanda masu murabus suna yi wa hukumar fansho zanga-zanga

Taron wanda ya samu halartar shugabannin tsaron jihar, shugabannin gargajiya, shugabannin siyasa da manyan malaman addinin da suke fadin jihar da sauran su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel