NDDC Ta Zama Saniyar Tatsa Ga ’Yan Siyasa, In Ji Gwamna Wike

NDDC Ta Zama Saniyar Tatsa Ga ’Yan Siyasa, In Ji Gwamna Wike

  • Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, ya ce ‘yan siyasan Najeriya sun mayar da hukumar bunkasa Niger Delta, NDDC sanuwar tatsar su
  • Gwamna Wike ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da SPU din barikin ‘yan sanda a Omagwa dake karamar hukumar Ikwerre a jihar ranar Talata 28 ga watan Satumba
  • A cewar sa ‘yan siyasa su na tururuwar zama darektan hukumar na bangaren kudi da kwangila saboda su na samun kudade masu tarin yawa

Jihar Ribas - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya ce hukumar bunkasa Niger Delta ta zama saniyar tatsar ‘yan siyasa a kasar nan.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taro na kaddamar da SPU a barikin ‘yan sanda a Omagwa da ke karamar hukumar Ikwerre da ke jihar a ranar Talata, 28 ga watan Satumba kamar yadda LIB ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa kan ta tuba, aure ya mutu

NDDC Ta Zama Saniyar Tatsa Ga ’Yan Siyasa, In Ji Gwamna Wike
Nyesome Wike, Gwamnan JIhar Rivers. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Kamar yadda Wike ya ce:

“NDDC ta zama sanuwar tatsar ‘yan siyasa. Sai ka ga ana tururuwar neman mukamin darektan hukumar gabadaya, ko darektan fannin kudi da na kwangila.
“Wadannan ne mutanen da suke samun kudin yin harkokin siyasa. Akwai ‘yan kwangila a Abuja shiyasa za ka ga darektan kullum ya na ziryar zuwa Abuja.”

Wike ya bayyana matsalolin NDDC

Kamar yadda LIB ta ruwaito, Wike ya bayyana cewa matsalolin NDDC ba yankin Niger Delta kadai bane, na gaba daya Najeriya ne.

“Ya buga misali da alkawarin da ministan ma’aikatar harkokin Niger Delta, Godswill Akpabio ya yi wanda ya ce NDDC zata canja don yin abubuwan da su ka dace ga yankin, Wike ya ce lokacin kaddamar da wannan aikin ya yi.

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

“Na kai NDDC kotu, kuma mun samu nasara akan su. Ka shigo jihar mutum, ba ka san tsarin ci gaban jihar ba amma har ka fara lalata tsarin jihar.
“Titin da kake so ka yi ba naka bane. Ba za ka natsu ka hada kai da jihar ba don jin wanne aiki jihar take bukata ba?
“Idan ka tambayi jihohi 9 da suke karkashin Niger Delta, kace jiha ta kaza, me kuke so NDDC ta yi muku? Bama son sanin ko wanene dan kwangilar. Mu aiki kawai muke so.”

Abin da yasa Abacha har abada zai cigaba da zama jarumi a jihar mu, Gwamnan PDP na Kudu

A wani labarin daban, Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa, a ranar Litinin, 27 ga watan Satumba ya bayyana marigayi Janar Sani Abacha, tsohon shugaban kasa na mulkin soja a matsayin jarumi na jihar Bayelsa.

Diri ya ce tsohon shugaban kasar ya samu wannan darajar ne saboda nan take da alkalami, marigayin, shekaru 25 da suka gabata (1996) ya kirkiri jihar ta Bayelsa kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yadda kasar Ghana ke damfarar ‘yan Najeriya ta hanyar Korona, 'yan majalisa

Gwamnan na jihar Bayelsa ya mika godiyarsa ga marigayin shugaban wanda ya amince a kirkiri jihar da ke da kananan hukumomi takwas a lokacin wanda ya ce ya gaza adadin da kundin tsarin mulki ya tanada, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel