Abinci Kamar Na Akuya: Mahaifiyar Ighalo Bayan Ya Kawo Mata Abincin Zamani a Jirgi

Abinci Kamar Na Akuya: Mahaifiyar Ighalo Bayan Ya Kawo Mata Abincin Zamani a Jirgi

  • Odion Ighalo ya na ci gaba da kyautata wa mahaifiyar sa kamar yadda ya saba, ya wallafa wani bidiyon ta a shafin sa na Instagram
  • An hango mahaifiyar tasa wacce ta manyanta tana nuna rashin jindadin abincin da aka gabatar ma ta a jirgi
  • Kamar yadda ta nuna an gabatar mata da abincin zamani ne wanda ta nuna cewa bai dace da shekarun ta ba kuma bai kayatar da ita ba

Mahaifiyar fitaccen dan kwallon kafar Najeriya, Odion Ighalo ta nuna takaicin ta akan gabatar ma ta soyayyen dankalin turawa da wani tumatir mai dandano a cikin jirgin sama.

Kowa ya san yadda iyayen mu na Najeriya su ka fi son abincin gargajiya, don haka gabatar wa mahaifiyar dan kwallon abincin zamani bai yi mata dadi ba.

Kara karanta wannan

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa kan ta tuba, aure ya mutu

Abinci Kamar Na Akuya: Mahaifiyar Ighalo Bayan Ya Kawo Mata Abincin Zamani a Jirgi
Mahaifiyar Ighalo ta ce bata gamsu da abincin zamani na jirgin sama ba: Photo: ighalojude
Asali: Getty Images

Kamar yadda LIB ta ruwaito, Ighalo ya wallafa bidiyon yadda mahaifiyar sa take nuna rashin jin dadin ta game da abincin zamanin da aka gabatar mata, yayin da take korafi da turanci, inda take cewa:

“Ba na iya cin wannan abinci.”

Kamar yadda ya wallafa a shafin sa na kafar sada zumuntar zamani ta Instagram, mahaifiyar sa ta nuna farantin abincin inda aka zuba sarrafaffen tumatirin mai dandano tana cewa:

“Akuya ce kadai take cin ganye. Babu wani abu a cikin wannan banda tumaturai guda biyu.”

Dankalin turawa abinci ne wanda jiragen saman Turai su ke gabatar wa manyan mutane da hamshakan ‘yan kasuwa a jirgi musamman idan za su yi tafiya mai tsawo.

Irin abincin da aka gabatar mata, ana soya dankalin turawan da aka yanke a tsaitsaye ne kwarai da man gyada sannan aka hada da wani tumatur na musamman don ya kara armashi.

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Abin da yasa Abacha har abada zai cigaba da zama jarumi a jihar mu, Gwamnan PDP na Kudu

A wani labarin daban, Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa, a ranar Litinin, 27 ga watan Satumba ya bayyana marigayi Janar Sani Abacha, tsohon shugaban kasa na mulkin soja a matsayin jarumi na jihar Bayelsa.

Diri ya ce tsohon shugaban kasar ya samu wannan darajar ne saboda nan take da alkalami, marigayin, shekaru 25 da suka gabata (1996) ya kirkiri jihar ta Bayelsa kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Gwamnan na jihar Bayelsa ya mika godiyarsa ga marigayin shugaban wanda ya amince a kirkiri jihar da ke da kananan hukumomi takwas a lokacin wanda ya ce ya gaza adadin da kundin tsarin mulki ya tanada, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel