Abin da yasa Abacha har abada zai cigaba da zama jarumi a jihar mu, Gwamnan PDP na Kudu
- A ranar Litinin 27 ga watan Satumba ne aka bawa tsohon shugaban kasa na soja, Janar Sani Abacha lambar yabo
- Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, ya bayyana tsohon shugaban kasar na mulkin soja a matsayin gwarzo a jihar Bayelsa
- Diri, yayin bikin cikar jihar Bayelsa shekaru 25 da kafuwa, ya ce Abacha ya kirkiri jihar ne a lokacin da wasu da dama ba su so ba
Bayelsa - Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa, a ranar Litinin, 27 ga watan Satumba ya bayyana marigayi Janar Sani Abacha, tsohon shugaban kasa na mulkin soja a matsayin jarumi na jihar Bayelsa.
Diri ya ce tsohon shugaban kasar ya samu wannan darajar ne saboda nan take da alkalami, marigayin, shekaru 25 da suka gabata (1996) ya kirkiri jihar ta Bayelsa kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gwamnan na jihar Bayelsa ya mika godiyarsa ga marigayin shugaban wanda ya amince a kirkiri jihar da ke da kananan hukumomi takwas a lokacin wanda ya ce ya gaza adadin da kundin tsarin mulki ya tanada, Daily Trust ta ruwaito.
Diri ya ce akwai yiwuwar Abacha ba shi da farin jini a cikin jerin shugabannin Nigeria amma jarumi ne a Bayelsa kuma zai cigaba da kasancewa hakan har abada.
Kalamansa:
"Ina son yin amfani da wannan damar in gode wa mutum daya. Ta yiwu ba shi da farin jini a Nigeria, amma a wuri na da 'yan Bayelsa, muna masa kallon mutum mai daraja, jarumi. Mutumin da ya yi amfani da alkalami, ya rattaba hannu aka kirkiri Jihar Bayelsa. Ina magana ne kan marigayi Janar Sani Abacha.
"Muna girmama shi a matsayin mu na jiha da al'umma. Da saka hannunsa shi kadai, ya kirkiri jiha mai kananan hukumomi takwas kacal, wadda hakan bai kai adadin da kundin tsarin mulki ya tanada ba."
A yunwace jama’a suke, ka yi wani abu kafin su yi wani abu, Dino Melaye ga Shugaba Buhari
A wani labarin daban, Sanata Dino Melaye ya yi wata wallafa ta shafin sa na kafar sada zumuntar zamani ta Instagram yana bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara.
Kamar yadda LIB ta ruwaito, ya bukaci shugaba Buhari ya yi gaggawar tallafa wa mutanen Najeriya sakamakon bakar yunwar da take addabar su.
Asali: Legit.ng