Babbar Magana: Wata mata ta shararawa jami'in dan sanda mari a Caji Ofis

Babbar Magana: Wata mata ta shararawa jami'in dan sanda mari a Caji Ofis

  • Wata kotu dake zamanta a Ikeja, babban birnin jihar Lagos, ta garkame wata mata yar kimanin shekara 55 bisa zargin faɗa da ɗan sanda
  • Maria Taiwo, ta tafka wa wani sajan ɗin yan sanda mari yayin da suke gardama a caji ofis biyo bayan kame ɗan ta da suka yi
  • Sai dai kotun ta bada belin matar a kan kuɗi naira dubu N100,000, sannan kuma ta ɗage sauraron ƙarar zuwa watan Nuwamba

Lagos - Kotun majistire dake zamanta a Ikeja, jihar Lagos, ta garkame wata mata yar kimanin shekara 55, Maria Taiwo, bisa zargin ta da marin jami'in ɗan sanda, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Yan sanda sun gurfanar da Taiwo mai sana'ar gyaran gashi a 23, Calvary St., Obawole, Ogba, Lagos, a gaban kotun kan zargin tada yamutsi da cin mutuncin ɗan sanda.

Read also

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Kotu ta ɗaure wata mata saboda matin ɗan sanda
Babbar Magana: Wata mata ta shararawa jami'in dan sanda mari a Caji Ofis Hoto: vanguardngr.com
Source: UGC

Mai shigar da kara, ƙaramin sufetan yan sanda, Olusegun Oke, ya shaidawa kotu cewa matar ta aikata laifin ne ranar 31 ga watan Agusta a caji ofis ɗin Ogba.

Meyasa matar ta aikata haka?

Bugu da ƙari, Oke ya faɗawa kotu cewa matar ta aikata haka ne a caji ofis ɗin da ake tsare da ɗan data haifa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace cece-kuce ya ɓarke tsakanin matar da ɗaya daga cikin jami'an yan sandan ofishin, Sajan Ameh Elijah.

Laifin da Taiwo ta aikata, a cewar mai shigar da kara, ya saɓa wa kundin dokokin dake kunshe a sashi na 168 da 170 na dokikin aikata manyan laifuka a jihar Lagos.

Sai dai a nata ɓangaren, wacce ake ƙara, Maria Taiwo, tace sam ba ta aikata laifin da ake zarginta da shi ba.

Wane mataki Kotu ta ɗauka?

Read also

Gwarazan Yan Sanda Sun Ragargaji Yan Bindiga Yayin da Suka Yi Kokarin Kai Hari Zariya, Sun Damke 5

Majistire D.S Odukoya, ya baiwa wacce ake ƙara damar beli a kan kuɗi kimanin dubu N100,000.

Daga nan kuma sai Odukoya ya sanar da ɗage ƙarar har zuwa 3 ga watan Nuwamba, 2021.

A wani labarin kuma Yan Najeriya ba zasu iya rayuwa shekara 40 cikin kangin talauci ba, PDP ta caccaki Sheriff

Bababar jam'iyyar hamayya PDP ta maida martani ga kalaman tsohon gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff.

Sheriff, wanda ke shirin neman takarar zama shugaban jam'iyyar APC, yace suna fatan jam'iyyar APC ta zarce shekaru 40 tana mulkin Najeriya.

Source: Legit.ng

Online view pixel