Yan Najeriya ba zasu iya rayuwa shekara 40 cikin kangin talauci ba, PDP ta caccaki Sheriff
- Bababar jam'iyyar hamayya PDP ta maida martani ga kalaman tsohon gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff
- Sheriff, wanda ke shirin neman takarar zama shugaban jam'iyyar APC, yace suna fatan jam'iyyar APC ta zarce shekaru 40 tana mulkin Najeriya
- PDP tace ya kamata Sheriff ya farka daga baccin da yake, domin yan Najeriya sun riga da sun dawo daga rakiyar APC
Abuja - Jam'iyyar hamayya PDP ta faɗawa tsohon gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff, cewa ya daina mafarkin APC zata cigaba da mulki har na tsawon shekara 40, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.
Jam'iyyar PDP, yayin da take martani kan kalaman Sheriff, ranar Litinin, ta hannun sakataren watsa labaranta, Kola Ologbondiyan, tace yan Najeriya sun riga sun dawo daga rakiyar APC.
A cewar PDP, yan Najeriya sun riga da sun gano APC da muƙarrabanta na da hannun a zubar da jini, kashe-kashe, rikici, cin hanci da rashawa da kuma matsin tattalin arziki, sabida haka ba zasu amince ta zarce 2023 ba.
Shin yan Najeriya sun shirya kayarda APC?
Wani sashin martanin PDP, yace:
"Ya kamata Sheriff ya san cewa yan Najeriya na sane da halin ƙakanikayi da jam'iyyar APC da mambobinta suka jefa su."
"Hakanan kuma sun san gaskiyar abinda ya kawo yawaitar ayyukan ta'addanci, yan bindiga, satar kuɗin gwamnati, take hakkin al'umma da kuma maguɗin zaɓe a ƙasa, duk wannan na faruwa ne ƙarƙashin APC."
"Yan Najeriya sun shirya watsad da APC a babban zaɓen 2023, kuma babu wani maguɗi ko manaƙisar da zata hana tabbatar da cewa APC bata ƙara kwana ɗaya ba a gaban 29 ga watan Mayu, 2023."
Saboda haka, jam'iyyar PDP ba zata ce komai ba sai tausayawa Ali Modu Sheriff da sauran abokanan tafiyarsa domin matsalar da ta addabi ƙasar nan ta zo ƙarshe, kamar yadda this day ta ruwaito.
A wani labarin kuma Babu ranar daina satar jarabawa a Arewa sai an yi abubuwa biyu, Farfesa Salisu Shehu
Shugaban jami'ar Al-Istiqama dake jihar Kano, Farfesa Salisu Shehu, yace babu ranar daina satar jarabawa a arewa har sai an ɗauki matakai.
Babban malamin addinin yace al'ummar Arewa sun lalace ta yadda basu damu da wace hanya aka bi ƴaƴansu suka samu sakamakon jarabawa ba.
Asali: Legit.ng