Hotunan budurwar da ta rasu ana sauran mako 5 aurenta sun gigita jama'a

Hotunan budurwar da ta rasu ana sauran mako 5 aurenta sun gigita jama'a

  • Kawaye, abokai, 'yan uwa da abokan arziki sun fada tashin hankali bayan wata amarya ta rasu ana sauran mako 5 bikin ta
  • An gano cewa, Alice wacce za ta yi aure da angon ta a watan Oktoba ta rasu sa'o'i kadan daga fara rashin lafiya
  • Kamar yadda wani dan uwan angon ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya jajanta tare da bayyana katin aurensu

Adamawa - 'Yan uwa da abokan arziki sun fada cikin damuwa da tsananin alhini bayan mutuwar wata budurwa ana saura mako 5 aurenta a jihar Adamawa.

Marigayiyar wacce aka gano sunanta Alice Liman da saurayinta, Kadama Birgamus, sun shirya tsaf domin yin aure a karamar hukumar Yola ta kudu a ranar 30 ga watan Oktoban 2021.

Read also

Kaduna: 'Yan bindiga sun kai farmaki coci, sun sheke mai bauta

Hotunan budurwar da ta rasu ana sauran mako 5 aurenta sun gigita jama'a
Hotunan budurwar da ta rasu ana sauran mako 5 aurenta sun gigita jama'a. Hoto daga Samuel Nathaniel Mombol
Source: Facebook

Bayanai kan mutuwar ta har yanzu ba su da yawa duk da an ce ta rasu ne bayan sa'o'in kadan da wani ciwo ya kama ta.

Wani Samuel Mombol, wanda tun farko ya wallafa katin gayyatar auren a shafinsa na Facebook, ya yi fatan auren ya kasance cike da jin dadi.

Daga bisani kuwa, ya sake yin wata wallafa a ranar Lahadin da ta gabata inda ya ke sanar da mummunan al'amarin

"Duk da abun takaici ne a bangarenmu da muka rasa amaryarmu, mun saka tawakkali ga Ubangiji a komai. Muna yi wa 'yan uwan ta ta'aziyya da kuma dan uwanmu Kadams Birgamus," ya rubuta.

'Yan bindiga sun kallafa wa manoman jihar Katsina haraji

A wani labari na daban, sakamakon hauhawar ta’addanci a fadin jihar Katsina, manoma da dama sun hakura da noma gonakin su sakamakon yadda ‘yan bindiga suka tilasta musu biyan harajin gonakin su.

Read also

Kwana 5 da mutuwar Mailafia, ba bu saƙon ta’aziyya daga Buhari da El-Rufai

Kamar yadda gwamnatin jihar Katsina ta kiyasta, gonaki 5,884 wadanda da ake noma wa aka dena saboda farmakin da ake kaiwa gonakin akai-akai.

Daga watan Janairu zuwa Yunin 2021 kamar yadda gwamnatin jihar ta bayyana, an dakatar da noma hectare 23,333 na gonaki 2,924.

A karamar hukumar Danmusa a kauyen Gurzar-Kuka, Mara, Dunya da sauran kauyaku da ke kusa da dazuka suna fama da biyan haraji ga ‘yan bindiga idan za su yi anfani da gonakin su.

Source: Legit

Online view pixel