Da duminsa: Babban bankin Najeriya ya kaddamar da shafin yanar gizo na E-Naira

Da duminsa: Babban bankin Najeriya ya kaddamar da shafin yanar gizo na E-Naira

  • Babban bankin Najeriya ya kaddamar da shafin kudin kasar na yanar gizo mai suna E-Naira
  • Kamar yadda daraktan yada labarai na CBN, Osita Nwanisobi ya sanar, an bude shi a yau Litinin
  • Sai dai kuma, duk da bude shi da aka yi, ba za a fara cinikayya ba sai an kaddamar a ranar 1 ga Oktoba

FCT, Abuja - Babban bankin Najeriya, CBN, ya kaddamar da shafin yanar gizo na e-naira kafin a kaddamar da shi a hukumance ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa.

Daily Trust ta ruwaito cewa, shafin ya fara aiki amma har yanzu ba a fara harkar cinikayya da shi ba.

Babban bankin Najeriya ya saki shafin mai adireshi www e-naira.com a ranar Litinin.

Read also

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Shinkafi Bayan Tura Wasiƙa, Sun Kutsa Ofisoshin 'Yan Sanda Sun Saci Bindigu

Daraktan yada labarai na babban bankin, Osita Nwanisobi, ya tabbatar da wannan cigaban ga manema labarai.

Da duminsa: Babban bankin Najeriya ya kaddamar da yanar gizo na E-Naira
Da duminsa: Babban bankin Najeriya ya kaddamar da yanar gizo na E-Naira. Hoto daga dailytrust.com
Source: UGC

Ya tabbatar da cewa, duk da shafin ya fara aiki, babu wata harkar cinikayya da aka aminta da farawa a kai har sai ranar 1 ga watan Oktoban 2021.

Tunin shafin ya samu maziyarta sama da miliyan daya a halin yanzu.

Dubawar da Daily Trust ta yi wa shafin ya nuna cewa, bayanan ayyuka ne kadai a shafin.

Amma kuma an bukaci masu ziyartar shafin da su sauke manhajar a wayoyinsu.

Ali Modu Sheriff: Muna fatan APC ta rike madafun iko na tsawon shekara 50

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, ya ce jam'iyyar jiga-jigan 'ya'yan jam'iyyar dole ne su yi aiki tare da gina wa jam'iyyar gadar da za ta tabbatar da ita a madafun iko har nan da shekaru 50, Daily Trust ta ruwaito.

Read also

Yadda ni da Sanusi II muka rike darajar Naira na tsawon shekara 5 a CBN inji Farfesa Moghalu

A yayin jawabi ga manema labarai a ranar Lahadi a Abuja, Sheriff, wanda yayi Sanata sau uku kuma mai neman kujerar shugabancin jam'iyyar na kasa, ya ce dole ne masu ruwa da tsakin jam'iyyar su hada kai wurin tabbatar da jam'iyyar ba ta tashi aiki ba bayan kammalar mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023.

Tsoffin gwamnoni da wasu jiga-jigan 'ya'yan APC sun fara neman hanya tare da neman darewa kujerar shugabancin jam'iyyar ana tsaka da cece-kuce kan yankin da za a bai wa, Daily Trust ta wallafa.

Source: Legit

Online view pixel