'Yan Bindiga Sun Kai Hari Shinkafi Bayan Tura Wasiƙa, Sun Kutsa Ofisoshin 'Yan Sanda Sun Saci Bindigu

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Shinkafi Bayan Tura Wasiƙa, Sun Kutsa Ofisoshin 'Yan Sanda Sun Saci Bindigu

  • 'Yan bindiga sun kai hari a garin Shinkafi na jihar Zamfara a yammacin ranar Alhamis
  • Wani mazaunin garin ya tabbatar da harin inda ya ce sun kutsa caji ofis sun saci makamai
  • Ba a samu ji ta bakin kakakin 'yan sandan jihar Zamfara ba saboda toshe layukan waya a jihar

Jihar Zamfara - 'Yan bindiga, a ranar Alhamis, da yamma sun kai hari garin Shinkafi, inda har suka kutsa ofisoshin 'yan sanda suna ta harbe-harbe yayin harin kamar yadda Daily Trust Saturday ta ruwaito.

Rahoton ya ce maharan sun sace bindigu da dama yayin da suka kai harin ofishin 'yan sandan.

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Shinkafi, Sun Kutsa Ofisoshin 'Yan Sanda Sun Saci Bindigu
'Yan Fashin Daji. Hoto: Daily Trust/Bulama
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

An kama ma’aurata kan kashe dansu tare da binne shi cikin sirri saboda ‘rashin ji’

Kawo yanzu ba a kammala samun cikaken bayani ba, duba da cewa Shinkafi na cikin garuruwan da aka datse wayar tarho sun farkon wannan watan kamar yadda jami'an tsaro suka bukata.

Wani mazaunin Shinkafi ya tabbatar da afkuwar harin

Rahoton na Daily Trust ya ce wani mazaunin garin da ya yi magana daga Sokoto ya tabbatar da harin a kafar sada zumunta a safiyar ranar Juma'a.

Ya ce maharan dauke da makamai sun iso garin a lokacin mutane suna sallar magariba suka shafe kimanin awa daya suna abin da suke so.

Maharan sun turo wasika kafin zuwarsu

Majiyar ya ce harin ya zo ne kwana daya bayan aike wa garin wasikar barazanan kawo hari, inda shugabannin 'yan bindiga Kachalla Turji da Halilu Sububu suka hada kai don kai hari a Shinkafi da kewaye.

Shinkafi ce babban gari da ya hada Zamfara da jihar Sokoto. A baya, yan bindiga sun ta kai hare-hare a garin.

Kara karanta wannan

Yunwa ta fara fatattakar 'yan bindiga daga jihar Katsina, inji gwamna Masari

Ba a samu nasarar tuntubar kakakin 'yan sandan jihar Zanfara ba saboda toshe hanyar sadarwa, yayin da kakakin yan sanda na kasa, CP Frank Mba ya ce bai da masaniya game da harin.

'Yan bindiga sun afka ofishin ƴan sandan Zamfara, sunyi kisa, sun sace bindigu AK-47 masu yawa

A wani labarin daban, wasu ɓata gari da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne sun kai hari ofishin yan sanda a Zamfara sun kashe jami'in ɗan sanda ɗaya, rahoton SaharaReporters.

Yan bindiga sun kuma kashe wani shugaban ƴan banga da wasu mutane biyu a garuruwan Nahuce da Gidan Janbula a ƙaramar hukumar Bungudu.

Har wa yau, ƴan bindigan sun yi awon gaba da mutane hudu yayin da suka kawo harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164