Atiku ba dan Najeriya bane: An dage karar da ke neman hana Atiku tsayawa takara

Atiku ba dan Najeriya bane: An dage karar da ke neman hana Atiku tsayawa takara

  • Kotu ta yi zama kan bukatar a hana Atiku tsayawa takarar shugaban kasa 2023, an kuma dage kara
  • Rahotanni sun bayyana cewa, an dage karar ne bisa gazawar bangaorori wajen bijiro da wasu bayanai
  • Wata kungiya ce ta shigar da Atiku kara kan cewa shi ba dan Najeriya, don haka bai cancanci tsayawa takara ba

Abuja - Wani rahoto da jaridar The Nation ta fitar ya nuna cewa an dage karar da ke neman kalubalantar cancantar tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar na tsayawa takarar shugaban kasan Najeriya a ranar Litinin, 27 ga watan Satumba.

A cewar mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja, hakan ya faru ne saboda gazawar bangarorin karar wajen daidaita tsare-tsaren da aka yi musu kwaskwarima don karbar wanda ake kara na 5.

Read also

2023: Jiga-jigan PDP na Arewa sun dage kan tikitin takarar shugaban kasa

Kotu ta dage karar da ke kalubalantar cancantar Atiku na tsayawa takarar shugaban kasa
Tsohon mataimakin shugaban kasa | Hoto: bbc.com
Source: UGC

Vanguard ta kara da cewa alkalin a hukuncin da ya yanke ya dage shari'ar har zuwa ranar 6 ga watan Disamba don ci gaba da shari'a.

Idan za a iya tunawa, gamayyar Incorporated Trustees of Egalitarian Mission for Africa (EMA) sun yi karar Atiku ba haifaffen Najeriya bane, don haka bai cancanci tsayawa takara a Najeriya ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kungiyar ta sanya tsohon mataimakin shugaban kasa da kuma jam'iyyar PDP, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da Babban Lauyan Tarayya (AGF) a matsayin wadanda ake kara na 1 zuwa 4.

Yanzu-Yanzu: PDP ta nemi gwamnan CBN Godwin Emefiele ya gaggauta barin ofis

A wani labarin, Jam’iyyar PDP ta bukaci gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele yayi murabus cikin gaggawa, Daily Trust ta ruwaito.

Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP na Kasa, Kola Ologbondiyan ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Alhamis 23 ga watan Satumba a Sakateriyar Jam’iyyar ta Kasa da ke Abuja.

Read also

Jerin lokuta 5 da tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku yayi takarar kujerar shugaban kasa

Ya ce lokacin Emefiele a matsayin Gwamnan Babban Bankin CBN a karkashin gwamnatin APC ya gamu da gazawar manyan tsare-tsare na kudi, inda PDP ta bukaci ya bar ofishinsa na gwamnan CBN cikin gaggawa.

Source: Legit.ng

Online view pixel