2023: Jiga-jigan PDP na Arewa sun dage kan tikitin takarar shugaban kasa

2023: Jiga-jigan PDP na Arewa sun dage kan tikitin takarar shugaban kasa

  • Rashin jituwa na kunno kai a cikin Jam’iyyar PDP kan batun rigingimun rabon mukamai da ake fama da su
  • Rahotanni sun ce jiga-jigan jam'iyyar PDP daga arewacin Najeriya sun dage kan mika tikitin takarar shugaban kasa ga yankin
  • Jiga-jigan sun riga sun ɗauki matsayar kuma a shirye suke su matsa lamba ga jam'iyyar don ta amince da matsayin su

FCT, Abuja - Rahoton da jaridar Tribune ta wallafa ya nuna cewa jiga -jigan arewa a jam'iyyar PDP, suna ta faman neman goyon baya don samun tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar gabanin babban zaben 2023.

A cewar rahoton, shugabannin arewa a PDP sun gana a ranar Talata, 22 ga watan Satumba a Abuja don bayyana matsayinsu gabanin ganawar su da gwamnan jihar Enugu kuma shugaban kwamitin rabon takara na PDP, gwamna Ifeanyi Ugwuanyi.

Kara karanta wannan

Ba za mu tsayar da shugaba daga wata shiyya ba, kwamitin PDP ya magantu kan rabon kujerar shugaban kasa a 2023

2023: Jiga-jigan PDP na Arewa sun dage kan tikitin takarar shugaban kasa
2023: Jiga-jigan PDP na Arewa sun dage kan tikitin takarar shugaban kasa Hoto: PDP
Asali: Facebook

A cewar wata majiya da aka nakalto a cikin rahoton, taron a karkashin tsohon ministan harkokin 'yan sanda, Adamu Waziri ya samu halartar jiga-jigai 28 na babbar jam’iyyar adawa a fadin shiyyoyi uku da suka hada arewacin Najeriya.

Fiye da wakilai 6000 za su halarci babban taron PDP

A halin da ake ciki, jaridar Vanguard ta rahoto cewa sama da wakilai 6,000 za su hallara a Abuja don zaben sabon NWC a watan Oktoba na wannan shekarar, Gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa ya bayyana.

Fintiri wanda shi ne shugaban kwamitin shirya babban taron na kasa ya bayyana hakan ne a sakatariyar jam’iyyar, Abuja, a ranar Alhamis, 23 ga watan Satumba, jim kadan bayan kaddamar da kwamitocin kananan hukumomi 15 a wani biki da manyan jami’an jam’iyyar suka halarta.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta sake dage babban taron jam'iyya na jihohi zuwa wani lokaci

Ba za mu tsayar da shugaba daga wata shiyya ba, kwamitin PDP ya magantu kan rabon kujerar shugaban kasa a 2023

A gefe guda, kwamitin fito da yadda za ayi rabon kujeru na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Alhamis, 23 ga Satumba, ya ce ba shi da hurumin raba kujerun siyasa irin na shugaban kasa ko mataimakin shugaban Najeriya.

Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi, wanda kuma shine shugaban kwamitin, ya fadi hakan ne a cikin jawabinsa a yayin taron su na farko a gidan gwamnati, Enugu.

Legit.ng ta tattaro cewa shugabancin jam'iyyar ne ya kafa kwamitin domin rabawa shiyoyi kujerun PDP na kasa gabanin babban taronta da ake shirin gudanarwa a ranakun 30 da 31 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng