Yanzu-Yanzu: PDP ta nemi gwamnan CBN Godwin Emefiele ya gaggauta barin ofis

Yanzu-Yanzu: PDP ta nemi gwamnan CBN Godwin Emefiele ya gaggauta barin ofis

  • Jam'iyyar PDP ta bayyana bukatar gwamnan CBN ya bar ofis saboda barnar da ya yiwa kasa
  • PDP ta ce, APC da gwamnan su suka lalata darajar Naira a duniya, don haka kawai ya bar ofis
  • PDP ta fadi haka ne a yau Alhamis a Sakateriyar Jam'iyar da ke babban birnin tarayya Abuja

Jam’iyyar PDP ta bukaci gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele yayi murabus cikin gaggawa, Daily Trust ta ruwaito.

Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP na Kasa, Kola Ologbondiyan ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Alhamis 23 ga watan Satumba a Sakateriyar Jam’iyyar ta Kasa da ke Abuja.

Ya ce lokacin Emefiele a matsayin Gwamnan Babban Bankin CBN a karkashin gwamnatin APC ya gamu da gazawar manyan tsare-tsare na kudi, inda PDP ta bukaci ya bar ofishinsa na gwamnan CBN cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: AMCON ta ƙwace katafaren gidajen tsohon gwamnan Kwara Abdulfatah Ahmed

Yanzu-Yanzu: PDP ta nemi a gwamnan CBN Godwin Emefiele ya gaggauta barin ofis
Tutar jam'iyyar PDP | Hoto: vanguardngr.com

Ologbondiyan ya ce abin koyi ne a lura cewa lokacin da Emefiele ya hau kujerar Gwamnan Babban Bankin Najeriya a 2014 darajar Naira ta kasance N164 idan aka kwatanta da dalar Amurka.

A cewar Ologbondiyan:

“A yau, a hannun Emefiele da APC, Naira ta durkushe zuwa kusan N600 zuwa dala, ta durkusar da tattalin arzikin kasar nan.

Ya kara da cewa:

"A karkashin jagorancin Emefiele, CBN ta gaza a cikin babban aikinta na sarrafa tattalin arziki kuma ta nutse cikin yada farfaganda, tare da ikirarin da ba su nuna mummunan yanayin tattalin arziki da ake fama dashi ba."

Attahiru Jega da wasu manyan Najeriya sun kirkiri sabuwar jam'iyyar ceto Najeriya

Domin ciro Najeriya daga kangi, wasu fitattun ‘yan Najeriya sun kafa runduna ta uku mai suna Rescue Nigeria Project (RNP) gabanin zaben 2023.

Kara karanta wannan

FG ta ki halartar kotu don sauraran karar da Nnamdi Kanu ya shigar a kanta

Wadanda suka kafa RNP sun ce sun kaddamar da sabon tsarin siyasa ne domin baiwa 'yan Najeriya madadin jam'iyyar APC, da babbar jam'iyyar adawa ta PDP.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa wadanda suka kafa RNP sun hada da tsohon gwamnan jihar Kwara; Ahmed Abdulfatai, tsohon dan takarar shugaban kasa, Farfesa Pat Utomi, tsohon ministan ilimi; Farfesa Tunde Adeniran da tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke.

Sauran sun hada da tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta; Farfesa Attahiru Jega, tsohon mataimakin gwamnan jihar Kogi; Yomi Awoniyi, Sanata Lee Maeba, Dr Usman Bugaje, Ambasada Nkoyo Toyo, Yomi Awoniyi, Dr Rose Idi Danladi, da sauran su.

Rikici ya barke tsakanin gwamnoni biyu na APC saboda dokar hana kiwo a fili

A bangare guda, gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya caccaki takwaransa na jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, kan kalaman da ya yi game da dokar hana kiwo a fili.

Kara karanta wannan

APC za ta wargaje idan aka fito da ‘Dan takarar Shugaban kasa daga Arewa inji Okorocha

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Gwamna El-Rufai ya bayyana dokar hana kiwo a fili da wasu daga cikin gwamnonin kudu ke sanyawa a matsayin abin da ba zai yiwu ba.

Sai dai Gwamna Akeredolu a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Donald Ojogo ya fitar, ya ce bai kamata irin wannan magana ta fito daga shugaba ba, inji jaridar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel